HAUSA NEWSLabarai

Duniya na Allah-wadai da yunƙurin juyin mulki a Nijar.

Wani yuƙurin juyin mulki da ke faruwa a Jamhuriyar Nijar, ya fuskanci Allah-wadai daga ɓangarori daban-daban na duniya ciki har da Tarayyar Afirka da Majalisar Ɗinkin Duniya da kuma Amurka.

Tun da sanyin safiyar Laraba ne dakarun tsaron fadar shugaban ƙasa suke tsare da Shugaba Mohamed Bazoum a fadarsa da ke babban birnin Niamey.

Wata sanarwa daga fadar shugaban Nijar ta ce sojojin ƙasar za su kai hari a kan dakarun tsaron fadar Bazoum matuƙar ba su janye ba.

Rundunar sojojin ƙasar ga alama tana ci gaba da yin biyayya ga shugaban ƙasar kuma ba za a samu rahotannin ɓarkewar harbe-harben bindiga

Kafar yaɗa labaran gwamnatin ƙasar har yanzu tana ci gaba da yaɗa shirye-shirye; sai dai ba ta ambaci aukuwar wani yamutsi ba

Dakarun tsaro na musamman masu biyayya ga Shugaba Bazoum sun ja daga a zagayen gidan talbijin ɗin ƙasar da kuma fadar shugaban na Nijar.

Tarayyar Turai ta bayyana matakin sojojin a matsayin cin amanar ƙasa.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ce lamarin shi ne juyin mulki ko yunƙurin juyin mulki na tara cikin shekara uku kawai a Afirka ta Yamma da Afirka ta Tsakiya, yankin da a shekara goma ya yi namijin ƙoƙari don watsar da laƙabin da ake masa na “sashen juyin mulki”, kafin taɓarɓarewar tsaro babu ƙaƙƙautawa da cin hanci su sake buɗe ƙofa ga sojoji.

A shekarun baya-bayan nan an samu juyin mulki a Mali da Burkina Faso. Duka maƙwabtan na Nijar sun ba da umarni sojojin Faransa su fice daga cikin ƙasashensu kuma sun ƙulla ƙawance da Rasha.

Nijar, babbar abokiyar ƙawance ce ga Ƙasashen Yamma masu dama ciki har da Faransa da Amurka a yaƙi da ƙungiyoyin masu iƙirarin jihadi a Afirka ta Yamma.

Nijar ta yi fama da juyin mulkin sojoji har sau huɗu tun bayan samun ‘yancin kai daga Faransa a 1960

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button
error: Content is protected !!