Kannywood

Nurses Day: Kalli Shagalin Bikin Jarumi Daddy Hikima Abale Inda Aka Saka Kayan Asibiti

Shagalin Bikin Jarumin Kannywood Daddy Hikima Abale

Nurses Day: Kalli Shagalin Bikin Jarumi Daddy Hikima Abale Inda Aka Saka Kayan Asibiti.

An gabatar da Shagali na Karshe daya dauki Hankalin Mutane a bikin Adam Abdullahi Adam wanda akafi sani da Abale.

Kamar dai yadda kowa ya sani a ranar Juma’ar nan data gabata ne 27 ga watan January shekarar 2023 ne aka daura Auren Fitaccen jarumi a Masana’antar Kannywood watau Adam Abdullahi Adam.

Jaruman Kannywood da dama su samu hakartar wannan daurin Aure kuma sun nuna Kara wanda daga ciki akwai jarumi Adam Zango, Abubakar Bashir Maishadda, Yakubu Mohammad da Sauran su.

Bayan anyi duk Shagulgulan biki an gama sai kuma aka Gabatar da wani Shagalin na musamman wanda ya dauki Hankulan Mutane duba abune wanda ba’a saba yin irinsa ba watau “Nurses day”

An hango ango Abale acikin shiga irinta Ma’aikatan kiwon lafia duk da cewa dama Aikinsa ne amma abun yaja Hankalin Mutane.

Ga Vedio yadda Shagalin ya kasance nan kamar haka.

Related Articles

Back to top button