Kannywood

Yanzu Yanzu Kotu Ta Tura Murja Ibrahim Kunya Gidan Yari Akansu Aisha Izzar So Saboda…

Murja a Gidan Yari

Kotu ta aike da Murja Kunya zuwa gidan yari

Kotun shari’ar Muslunci da ke Filin Hoki a Kano ƙarƙashin mai Shari’a Abdullahi Halliru ta aike da Ƴar TikTok ɗin nan Murja Ibrahim Kunya zuwa gidan yari.

Lauya Barrister Lamiɗo Abba Soron Ɗinki ya karanto mata ƙunshin tuhume-tuhumen da ake mata wanda ta musanta.

Ana zargin Murja da ɓata suna da barazana ga Aisha Najamu ta Izzar So da kuma Ashiru Idris wanda dukanninsu abokananta ne.

Kotun ta ɗage sauraron ƙarar zuwa 16 ga watan Fabrairun da muke ciki.

Sai dai Lauyan Murja Barrister Yasir Musa ya nemi a tura ta zuwa Hisbah maimakon gidan Yari sai dai Kotun bata amince ba.

An gurfanar da shahrarriyar Ƴar TikTok ɗin nan Murja Ibrahim Kunya gaban Kotun shari’ar Muslunci dake Filin Hoki a jihar Kano a yau Alhamis, 2 ga watan Febrairu, 2023.

Murja Ibrahim Kunya gurfane gaban kotu

Ana zargin Murja da ɓata suna da barazana ga Aisha Najamu ta Izzar So da kuma Ashiru Idris wanda dukanninsu abokananta ne.

An karanto mata tuhumar da ake mata inda nan take ta musanta, daga nan ne kuma lauyanta, Barrister Yasir Musa, ya nemi a bada belinta, rahoton Freedom Rediyo.

Alkali mai Shari’a Abdullahi Halliru ya yi watsi da wannan bukata na lauyan Murja Ibrahim Kunya kuma ya bada umurnin jefa ta gidan ajiya da gyaran hali.

Lauyan Murja ya nemi a tura ta zuwa Hisbah maimakon gidan Yari amma Alkalin kotun ya sake watsa masa kasa a ido.

Kotun ta ɗage sauraron ƙarar zuwa 16 ga watan Fabrairu, 2023.

Related Articles

Back to top button