LabaraiSiyasa

2023: Na Shirya Tsaf Don Fara Fita Yakin Neman Zabar Tinubu Da Sauran ‘Yan Takarar APC –Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya baiwa jam’iyyar APC da ‘yan takararta tabbacin cewa a shirye yake ya yi wa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Bola Tinubu yakin neman zabe.

Buhari ya ce a shirye ya ke ya yi wa Tinubu yakin neman zabe da cikakken karfinsa.

Shugaban ya bayar da wannan tabbacin ne yayin da yake kawar da rade-rade kan damuwar cewa, ba a kara ganin shi ba a taron yakin neman zaben APC tun bayan kaddamar da taron yakin neman zaben na kasa a garin Jos na jihar Filato.

A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu ya fitar, ta ce shugaban kasar a lokacin da yake zantawa da al’ummar Nijeriya mazauna birnin Washington DC a ziyarar da ya kai kasar Amurka a kwanakin baya, ya ce “a shirye yake ya yi wa Jam’iyyar APC yakin neman zabe don ganin jam’iyyar ta yi nasara a babban zabe mai zuwa.”

Related Articles

Back to top button