LabaraiSiyasa

Aminu Adamu: Uwargida Aisha Buhari da Mutum 4 Za Su Bada Shaida a Kotu

Aminu Adamu: Uwargida Aisha Buhari da Mutum 4 Za Su Bada Shaida a Kotu

A cikin wadanda za su bada shaida a shari’ar ‘Yan sanda da Aminu Adamu har da Hajiya Aisha Buhari .

Mai dakin shugaban Najeriyan tana cikin shaidu biyar da jami’an tsaro za su gabatarwa Alkali a kotu.

Akwai wasu ‘Yan sanda da kotu za ta gayyata domin bada shaidar da za ta sa a kama matashin da laifi.

Mai dakin shugaban kasa, Aisha Buhari za ta gabatar da shaida a kan Aminu Adamu, wani dalibi da ake tuhuma da laifin ci mata zarafi a shafin Twitter.

Ana zargin Aminu Adamu a kotu da yin kalaman cin mutunci kan Aisha Buhari, Premium Times tace uwargidar shugaban kasa za ta yi bayani a gaban Alkali.

Wannan matashi mai shekara 24 wanda dalibi ne a jami’ar tarayya da ke Dutse a jihar Jigawa, ya fito yana cewa “Mama ta ci kudin talakawa, tayi bul-bul.’

Bayan kusan makonni biyu ana tsare da shi, jami’an tsaro sun gurfanar da Aminu a gaban Mai shari’a Yusuf Halilu na babban kotun tarayya mai zama a Maitama. An tsare Aminu a kurkuku Duk da ya ki amsa laifinsa, Alkali ya bukaci a cigaba da tsare dalibin a gidan gyaran hali na Suleja.

Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar A yau Alhamis ne za a cigaba da sauraron wannan shari’a, inda Lauyan wanda ake kara zai jira takardun jami’an ‘yan sanda domin ya nema masa beli a kotu.

Aisha Buhari za ta bada shaida

Jaridar tace daga cikin wadanda kotu za ta gayyata domin su bada shaida a kan karar da ake yi akwai ita Aisha Buhari wanda ake zargin an ci wa mutunci. Idan har matar shugaban kasar ta iya zuwa kotu, zai zama karon farko da ta bayyana a bainar jama’a, tun bayan da aka samu labari cewa ta samu rauni a kafa.

Wani wanda zai bada shaida a kotun shi ne Festus Jossiah, wanda yana cikin jami’an tsaron da suka je har jihar Jigawa, suka cafke dalibin da ake shari’a da shi. Sauran masu bada shaida daga bangaren wadanda suka shigar da kara sun hada da; Abdulsalam Zakari, Yahaya Njayo da Haliru Tahir, dukkansu ‘yan sanda ne. ‘Yan sanda suna tuhumar wannan yaro da laifin batanci wanda ya sabawa sashe na 391 na dokar ‘Penal Code’. Bayan sauraron bangarorin, za a yanke hukunci.

Ana neman beli An samu labari cewa Lauyan da yake kare wanda ake zargi da laifin cin zarafin Aisha Buhari yace suna neman beli saboda jarrabawar dalibin a jami’a. Wani malami a jami’ar tarayya ta Dutse da Aminu Adamu yake karatu, ya fadakar da jama’a cewa za a lalatawa matashi rayuwarsa idan har ya rasa jarrabawa.

Related Articles

Back to top button