Labarai

Amurka Ta Wallafa Sunayen Kasashe Masu Tauye Ƴancin Addini (Cikakken Jerin Sunaye)

Amurka Ta Wallafa Sunayen Kasashe Masu Tauye Ƴancin Addini (Cikakken Jerin Sunaye)

Amurka Ta Saki Sunayen Kasashe Masu Tauye Ƴancin Addini (Cikakken Jerin Sunaye)

Kasar Amurka ta fitar da sunayen wasu kasashen duniya da ta kira masu tauye hakkin addini. Sakataren Amurka, Antony Blinken ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar.

Amurka Ta Saki Sunayen Kasashe Masu Tauye Ƴancin Addini

Amma bayan shekara guda, an cire Najeriya daga jerin kasashen.

Binciken ya fitar da jerin sunayen kasashen bisa gwargwadon matakin abin da ake zarginsu da aikatawa.

Kasashen da ke take hakkin addini a cewar sanarwar ta Amurka sune.

1.Burma

2.Jamuhuriyar Al’ummar China (Sin) 3.Cuba

4.Eritrea

5.Iran

6.Nicaragua

7.DPRK

8.Pakistan

9.Rasha

10.Saudiyya

11.Tajikistan

12.Turkmenistan

Sunayen kasashe masu keta hakkin addini na musamman

1.Algeria

2.The Central African Republic

3.Comoros

4.Vietnam

Kungiyoyi da aka sa wa ido na musamman

1.Al-Shabab

2.Boko Haram

3.Hayat Tahrir al-Sham

4.Houthis

5.ISIS-Greater Sahara

6.ISIS-Afirka ta Yamma

7.Jama’ar Nusrat al-Islam wal-Muslimin

8.Taliban

9.The Wagner Group

Sanarwar da Antony Blinken ta kara da cewa: “Sanarwar da muka fitar na sunayen ya dace da al’adarmu da muradunmu na kare tsaron kasa da hakkan hakkin yan adam a duniya. Kasashen da ke kare hakkin bil adama sun fi zaman lafiya, kwanciyar hankali da cigaba kuma sune suka fi zama kawayen Amurka fiye da wadanda ba su yi kare hakokin.

“Za mu cigaba da sa ido kan yancin addini a kowanne kasar duniya tare da kare hakkin wadanda ake musgunawa saboda addininsu. Za kuma mu cigaba da tattaunawa da kasashen kan batun yancin addini ko suna jerin ko ba su ciki. “Muna maraba da dukkan gwamnatocin kasashe don tattaunawa kan dokoki da abubuwa da suka ci karo da dokokin kasa da kasa don cire su daga jerin.”

Related Articles

Back to top button