An Tsinci Gawar Wata Mace Cikin Dakin Wani Hotel A Sabon Garin Zariyan Jihar Kaduna
An Tsinci Gawar Wata Mace Cikin Dakin Wani Hotel A Sabon Garin Zariyan Jihar Kaduna

An rahoto cewa, hotel din na daya daga cikin wuraren da ake sauke mata masu zaman kansu don kama haya ta wucin gadi.
Wani mazauni a kusa da hotel din wanda ya bukaci a sayakaya sunansa, yace ana zargin matar wani abokin harkallar ta ne ya kashe ta bayan kwana biyu kafin a gano gawarta da misalin karfe 5:30 na safiyar ranar lahadi.
Majiyar ta ce, anji wani wari na fitowa daga dakin, inda lamarin ya ja hankalin jama’a aka gayyato jami’an ‘yansanda suka zo suka balle kofar dakin sika fito da gawawarta suka kai dakin ajiye gawarwaki na Asibitin koyarwa na ABU da ke Zaria.
Rahotanni sun ce, matar ‘yar asalin jihar Benuwai ce amma tana zaune ne a garin Zaria don yin karuwanci.
Sai dai an rahoto cewa, tuni jami’an ‘yansanda suka cafke mai kula da hotel din domin gudanar da bincike.