Labarai

Ba Zamu Daga Kafa Kan Malaman Addini Da Ke Kokarin Haddasa Rikici A Nijeriya Ba – DSS

Ba Zamu Daga Kafa Kan Malaman Addini Da Ke Kokarin Haddasa Rikici A Nijeriya Ba – DSS

Ba Zamu Daga Kafa Kan Malaman Addini Da Ke Kokarin Haddasa Rikici A Nijeriya Ba – DSS

A jiya Asabar ne hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta gargadi malaman addini na Musulunci da na Kirista da su daina tunzura ‘yan Nijeriya kan batanci ga gwamnati.

Rundunar ‘yan sandan sirrin ta kuma gargadi shugabannin siyasa da su daina amfani da ‘yan daba wajen gudanar da ayyukansu, inda ta bukaci matasa da kada su mayar da kansu karninkan ‘yan siyasa.

Babban daraktan hukumar ta DSS, Yusuf Bichi ne ya yi wannan gargadin a Abuja a yayin bikin yaye daliban leken asiri ta hukumar leken asiri ta 15 da aka gudanar a cibiyar nazarin harkokin tsaro ta kasa.

Bichi ya ce musamman masu yin kalaman batanci a kan Nijeriya ta yanar gizo da kuma sauran hanyoyi, ya kamata su yi la’akari da cewa kasar Nijeriya ba ta fuskantar mawuyacin kalubalen tsaro kamar yadda wasu suke bayyana ta.

Related Articles

Back to top button