Labarai

Ba Zamu Kara Wa’adin Daina Amfani Da Tsaffin Naira Ba Kuyi Hakuri Inji Gwamnati

Ba Zamu Kara Wa'adin Daina Amfani Da Tsaffin Naira Ba Kuyi Hakuri Inji Gwamnati

Gwamnan babban bankin Najeriya CBN, Mr Godwin Emefiele, ya bayyana cewa yan Najeriya suyi hakuri amma ba zai sauya ranar daina amfani da tsaffin takardun kudin Naira ba.

Emefiele ya bayyana hakan ne ranar Talata, 24 ga Junariu, 2023 bayan zaman MPC a birnin tarayya Abuja.

Ya bayyana cewa shi dai har yanzu bai ga dalilin da zai sa a kara wa’adin ba saboda an baiwa jama’a kwanaki 100 su mayar da kudadensu banki.

Ya ce ko shugaba Muhammadu Buhari ya fadi hakan sau biyu cewa duk mai kudin halal, kwanaki 100 sun isa ya mayar da kudadensa banki.

A rahoton ChannelsTv, Emefiele ya bayyana cewa:

“Gaskiya ayi hakuri bani da wani labari mai dadi ga wadanda ke son a dage ranar daina amfani da tsaffin kudi. Ina mai bada hakuri.”
“Dalili kuwa shine kamar yadda shugaban kasa ya fadi akalla sau biyu cewa kwanaki 100 ya isa ga kowa ya mayar da kudinsa banki.”
“Kuma mun dau duk matakan ganin cewa bankuna na bude don karban tsaffin kudin mutane. Kwanaki 100 sun isar gaskiya.”
“Mun bukaci bankuna su kara lokacin aiki kuma har ranar Asabar.”
“Babu wani dalilin da zai sa a dage sbaoda mutane sun ki mayar da tsaffin kudinsu baki.”

Related Articles

Back to top button
error: Content is protected !!