Labarai

Bidiyo: Innalillahi Yadda mummunar Gobara ta tashi a babbar kasuwar Maiduguri (Monday Market)

Gobarar Monday market dake Maiduguri

Innalillahi Yadda mummunar Gobara ta tashi a babbar kasuwar Maiduguri (Monday Market).

Wata gobara ta tashi a kasuwar da ake kira Kasuwar Litinin da ke birnin Maiduguri.

Gobarar, wadda rahotanni suka ce ta tashi ne a daren jiya ta yi ɓarnar da har yanzu ba a tantance ba.

Hotunan bidiyo da aka wallafa a shafukan sada zumunta sun nuna yadda hayaƙi ya turnuƙe sararin samaniyar birnin na Maiduguri sanadiyyar gobarar.

Wani ganau da BBC ta zanta da shi ya ce wutar na ci gaba da ci har zuwa safiyar Lahadi, inda mutane suka taru domin kai dauki.

Wani dan jarida da BBC ta tuntuɓa, Adamu Aliyu Ngulde ya ce mutane sun shiga cikin ruɗani saboda gobarar.

Related Articles

Back to top button