LabaraiSiyasa

Da Dumi-dumi: Bashir Machina Ya Sake Kayar Da Sanata Lawan a Kotun Daukaka Kara

Da Dumi-dumi: Bashir Machina Ya Sake Kayar Da Sanata Lawan a Kotun Daukaka Kara

A yau ne kotun daukaka kara dake zamanta a Abuja ta amince da takarar Sanata mai wakiltar Yobe ta Arewa a karkashin jam’iyyar APC, Hon. Bashir Sheriff Machina

Kotun daukaka karar ta tabbatar da hukuncin da babbar kotun tarayya da ke Damaturu ta yanke tun da farko wadda ta bayyana Bashir Machina a matsayin halastaccen dan takarar sanatan APC a Yobe ta Arewa.

Bugu da kari kuma, kotun ta yi watsi da karar da jam’iyyar APC ta shigar kan rashin amincewar da ta sanya daukaka karar.

Shugabar Kotun, Mai Shari’a Monica Dongban-Mensem wadda ta yanke hukuncin, ta ce babbar kotun tarayya da ke Damaturu ta yi gaskiya bisa tabbatar da zaben fidda gwani na majalisar dattawa wanda jam’iyyar APC ta gudanar ranar 28 ga watan Mayu da ya gabata, wanda ya bai wa Hon. Machina nasara tare da bai wa hukumar INEC ta sanya masa ido wajen aiwatar dashi.

  • Idan dai za a iya tunawa jam’iyyar APC mai mulki ta garzaya kotun daukaka kara tare da neman ayi watsi da hukuncin da babbar kotun tarayya da ke Damaturu ta yanke kana da bukatr a bayyana Ahmad Lawan a matsayin dan takarar sanata na jam’iyyar a Yobe ta Arewa.

Related Articles

Back to top button