Labarai

Dakta Olusola Saraki: Shekara 10 Da Rasuwar Dattijon Arziki, Baya Goya Marayu

Dakta Olusola Saraki: Shekara 10 Da Rasuwar Dattijon Arziki, Baya Goya Marayu

Dakta Olusola Saraki: Shekara 10 Da Rasuwar Dattijon Arziki, Baya Goya Marayu

 

Dakta Olusola Saraki: Shekara 10 Da Rasuwar Dattijon Arziki, Baya Goya Marayu   

A ranar Litinin 28 ga watan Nuwamba 2022 ne ‘yanuwa, iyalai da abokan siyasar Marigayi Dakta Abubakar Olusola Saraki (Turakin-Ilori) wanda aka fi sani da Oloye suka taru a babban dakin taro na Chida Otel da ke Abuja don tunawa da cika shekara 10 da rasuwarsa, an gudanar da taron ne a kakashin jagorancin Sarkin Musulmi Mai Martaba Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar 111 yayin da Sarkin Ilori Mai Martaba Alhaji Ibrahim Sulu-Gambari ya jagoranci tawagar Sarakunan gargajiyar da suka samu halartar taron, yayin da shaharren mai jawabin nan wanda ya shahara a Afrika, Farfesa P L O Lumumba ya gabatar da jawabi inda ya gabatar da mukala mai taken ‘Muhawarar A Kan Shugabanni Da Mabiya A Afrika’.

Sabon Salon da Taron Ya Dauka

Taron ya dauki wani sabon salo musamman ganin ana gudanar da shi ne a daidai lokacin da ake tsaka da gangamin tarukkan yakin neman zabe a sassan kasar nan na wadanda za su cike gurbin shugabanaci a shekarar 2023, amma maimakon masu shirya taron su mayar da dandalin taron ya zama tamkar wajen yakin neman zabe ko kuma wajen da za su tallata ‘yan takarar su amma sai gashi sun gaiyato kusan ‘yan siyasa daga dukkan bangarorin siyasar kasar nan, domin a hadu a kan akidar siyasar Marigayi Oloye ta kishin kasa da tabbagtar da cigaban ta.

A jawabinsa na maraba, daya daga cikin manyan ‘yan’yan Marigayi Sola Saraki, Tsohon shugaban majalisar Dattawa, Dakta Abubakar Bukola Saraki, ya bayyana cewa, dalilin wannan shi ne na ganin cewa, Marigayin yana da magoya baya da wadanda ya yi tasiri a rayuwarsu a kusan dukkan siyasun kasar nan a kan haka zai zama tamkar rashin mutunci gare shi a ware wasu ‘yan siyasa a irin wannan taron. Ya ce, Mahaifinsu ya rungumi al’umma daga dukkan bangarorin kasar nan ba tare da nuna banbacin addini ko kabilanci ba, “Wannan akidar ce ta sanya a kusan dukkan inda ka ambaci sunansa sai ka samu wanda zai bayar da shaidar wani abin alhairin da ya aikata tare da kuma yi masa addu’a, mu da kanmu iyalansa har yanzu muna cigaba da amfana da ayyukan alhairin da ya gabatar a zamanin rayuwarsa, za kuma mu cigaba da amfana har zuwa ‘ya’ya da jikokinmu, saboda haka muke kira ga al’ummar Nijeriya su rungumi halayya irin ta Dakta Abubakar Olusola Saraki ta haka za a samu kasa mai cike kwanciyar hankali da son juna.’’ In ji shi.

A nasa jawabin a matsayinnsa na shugaban taron, Sarkin Musulmi Alhaji Abubakar Sa’ad ya tuno da lokacin da ya fara saduwa da Marigayi Sola Saraki a lokacin yana aikin soja a mukamin Kaftin a barikin Soja da ke Ilori, ya ce, tun a lokacin ya fahinci mutunci da dattakunsa daga nan ne kuma suka kulla kyakyawar alaka da iyalan Marigayin har zuka wannan lokacin. Al’umma da dama na cigaba da kewar Marigayin ne saboda irin ayyyukan al’hairin da ya shuka wadanda suka hada bayar da tallafin karatu ga yaran talakawa da koya wa yaran talakawa sana’o’in dogaro da kai, wanda haka ya sa har zuwa yanzu sunansa bai bace a zukatan al’umma ba saboda yadda ya rike su a matsayin ‘ya’yansa. Daga nan ya shawarci zuriyyar da Marigayin ya bar a karkashin jagorancin Dakta Bukola Saraki, Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa da su tabbatar da sun rungumi akidun marigayyin, ‘Ta haka ne sunansa zai cigaba da wanzuwa” in ji shi.

A mukalar da ya gabatar, mai take “Muhawara a Kan Shugabanci da Magoya baya’ Farfesa LPO Lumumba ya yi dogon tsokaci ne a kan yadda Afrika ta fada cikin matsalar shugabanci da kuma yadda magoya baya suka kasa fahintar alhakin da ke kansu na tsayuwa tare da tsawata wa shugabanni a yayin da suka kauce hanyar da ya kamata na bunkasa rayuwar al’umma, ya ce, tun da farko Turawan Mulkin mallaka basu shirya barin tafiyar da harkokin mulkin kasashen Afrika ba, a kan haka suka dora kasashen a kan tafarkin da za su cigaba da tsoma baki a kan yadda ake tafiyar da harkokin kasa duk kuwa da sun bar mukin a hannun ‘yan kasashen Arikan ne a zahiri amma sune ke tsarawa sune kuma suke bayar da yadda za a gudanar da komai, a kan haka ne suka kafa kungiyoyi irin su na kasashe renon Birtaniya da irin na kasashe renon Faransa” in ji shi.

Ya ce, dole shugabannin Afrika a wananan lokaci su farka su kuma yi koyi da halaye irin su na Marigayi Sola Saraki wadanda suka sanya cigaban al’ummar su fiye da komai, “Ta hake ne kawai al’ummar kasashen Afrika za su kubuta daga kangin Turawan Mulki Mallaka duk kwa da sun ba kasashen mu mulkin kai fiye da shekaru 60 da suka wuce’, in ji shi.

An dai haifi Dakta Abubakar Olusola Saraki ne a a ranar 17 ga wata Mayu na shekarar 1933 ya auri Misis Florence Morenike Saraki suna da ‘ya’ya hudu, sun kuma hada da Dakta Abubakar Bukola Saraki Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa kuma tsohon Gwamnan Jihar Kwara har sau biyu da Sanata Rukayat Gbemisola Saraki wadda ta taba zama mamba a majalisar wakilai a halin yanzu kuma ita ce Ministar ma’adanai da Misis Fatimoh Temitope Edu (Nee Saraki) wadda a halin yanzu tana harkokin kasuwancinta ne a Legas sai kuma na karshe, Mista Mutairu Olaolu Saraki, wanda ya taba yi wa marigayi tsohon shugaban kasa Umaru Musa ‘Yar’adua mataimaki na musamman. Dakta Sola Saraki ya rasu ne a ranar 14 ga watan Nuwamba 2012 yana da shekara 79 a duniya.Cikin abubuwan da aka shiya don tunawa da cikarsa shekasra 10 da rasuwa, akwai bayar da tallafin magani kyauta ga mabukata a garin Ilori, kaddamar da littafin tarihinsa wanda aka sama suna ‘’Sola Saraki: The Stateman’’, littafin na kunshe ne da tarihin gwagwamayar rayuwarsa na siyasa da yadda ya yi watsi da aikinsa na Likita ya rungumi siyasa da mukaman da ya rike har zuwa lokacin da ya zama Jagoran Majalisar Dattawa a jamhoriyya ta 2, lokacin Alhaji Shehu Shagari ke mulki.

Taron ya samu halartar manyan ‘yan siyasa daga dukkan bangarorin siyasar kasar nan.

Related Articles

Back to top button