LabaraiSiyasa

Dalibin Da Ya Tsokani Aisha, Zai Gana Da Buhari A Villa

Dalibin Da Ya Tsokani Aisha, Zai Gana Da Buhari A Villa

Dalibin Da Ya Tsokani Aisha, Zai Gana Da Buhari A Villa

Bayan sakin dalibin nan Aminu Muhammad da ya tsokani uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari da cewa ta ci kudin talawa ta koshi zai gana da shugaba Buhari.

Aminu l, wanda dalibin Jami’ar Gwamntin Tarayya da ke Dutse ne, ya shiga hannun hukuma bisa zargin ba ta suna da ya yi wa matar shugaban kasa a shafin Twitter, wanda hakan ta kai sa ga zuwa gidan yarin Suleja da ke Jihar Neja.

Sai dai bayan janye karar da matar shugaban kasa ta yi, Aminu, ya kubuta kuma tuni alkali ya bayar da umarnin sakin shi.

Ana sa ran Aminu zai gana da shugaban kasa, Muhammadu Buhari kafin ya koma garinsu.

Mai daukar nauyin kula da Aminu, Kabiru Shehu, ne ya tabbatar da wannan matakin a hirarsa da Jaridar LEADERSHIP.

Ya ce yanzu haka Aminu yana fadar shugaban kasa da ke Aso Villa da ke Abuja, inda zaman jiran haduwa da shugaba Buhari.

Ya ce, “Mun ji dadi da farin ciki bisa wannan lamarin. Muna shaukin sake haduwa da dan uwanmu.”

Aisha dai ta janye karar da ta shigar da Aminu wanda hakan ne ya kawo ga wannan matakin bayan shan suka da caccaka daga wajen ‘yan kasa.

Lauyan Aminu, C.K Agu ya tabbatar da cewa matar shugaban kasa, ta janye tuhume-tuhumen da take yi wa Aminu.

Shi dai Aminu wanda dalibin ajin karshe ne ya wallafa hoton Aisha Buhari inda ya ce “Su mama an chi kudin talkawa an koshi” lamarin da ya fusata Aisha har ta sa aka kamo shi sannan aka gurfanar da shi a kotu.

Related Articles

Back to top button