LabaraiSiyasa

Dama Ta Karshe Ta Yadda Za’a Dakile Talauci Kafin Zaben 2023

Dama Ta Karshe Ta Yadda Za'a Dakile Talauci Kafin Zaben 2023

Dama Ta Karshe Ta Yadda Za’a Dakile Talauci Kafin Zaben 2023

Dama Ta Karshe Ta Yadda Za’a Dakile Talauci Kafin Zaben 2023

A tsarin dimokuradiyya, wanda shi ne tsarin shugabancin da ya fi dacewa da karbuwa a wajen jama’a.

‘Yan siyasa suna yi wa masu zabe alkawuran da za su yi idan sun sami nasara.

A bisa yarjejeniyar tsarin, masu zabe suna yin la’akari da abubuwan da suka amfana ko suka samu a lokacin da wa’adin ‘yan siyasa ya zo karshe.

Abu ne sananne ga ‘yan siyasa a lokacin da suka rike abin magana idan sun hau dandalin siyasa suna alkawuran samar da ingantaccen ruwan sha da gina hanyoyi da makarantu da inganta noma. Wadannan su ne alkawuran da ake yi wa talakawa, masu kudi da marasa kudi ko masu ilimi da marasa ilimi da duk dai wanda ake jagoranta.

A cewar Marigayi Malam Aminu Kano, masu rinjaye amma suka yi shiru ba sa iya magana, wato yawansu ba shi da amfani. Muddin suka kasance a tare da ‘yan siyasa, zai ba su damar samun nasarar zabe. Talakawa fa na son Shugaban kasa Muhammadu Buhari sosai da sosai.

A shekarar 2019, Shugaba Buhari ya yi alkawarin cewa zai fitar da mutum miliyan 100 daga kangin talauci kafin shekara ta 20230. Hakan na nuna cewa dole za a fitar da mutum miliyan 10 cikin talauci a shekarar 2020. Yanzu dai kasa da makonni 26 suka rage wa Buhari a mulki, wanda ake zaton dai wannan buri zai wuya a cimma shi. Abubuwa da dama sun taikama wajen kasa cimma wannan burin da aka tsara, wadanda suka hada da shiga kuncin rayuwa na matsin tatalin arziki da aka yi har karo biyu mabambanta, annoba da rashin tsaro da cin hanci rashawa da ciko da ake wa kasafin kudi da satar mai da rashin.

Hanyoyin Dakile Talauci

Turawa na cewa daukar abu baibai ga tsarin gwamnatin da ake zato zai iya ba ka daidai tsarin da ake bukata. A watan Nuwamba shekarar 2022, wani rahoton da hukumar kididdiga ta kasa (NBS) ta bitar ya nuna cewa kasar ta sanya mutum miliyan 5 cikin matsanancin talauci a duk shekara na tsawon shekara 6 a maimakon a fitar da su cikin talauci. A yanzu akwai mutum miliyan 133 da suke cikin tsananin talauci da kuncin rayuwa a Nijeriya, wanda ya kai kashi 62.9% na yawan ‘yan Najeriya kenan. A shekarar 2016, mutum miliyan 103 ne suke zaune cikin talauci kimanin kashi 53.7 na ya wan ‘yan Nijeriya kenan.

Hukumar NBS ta yi kira da a dauki matakin gaggawa don kare mutane da shiga cikin kuncin rayuwa da kuma a kare su daga talauci.

 

Related Articles

Back to top button