Labarai

Dan Najeriya Ya Gina Bandaki Mai Samar Da Iskar Das Don Girki Da Wutar Lantarki

Dan Najeriya Ya Gina Bandaki Mai Samar Da Iskar Das Don Girki Da Wutar Lantarki

A yayin da mutane ke kokawa kan karuwar kudin iskar gas a kasar, wani dan Najeriya ya samo zabi.

Mutumin ya gina bandaki da ke samar da iskar gas tare da lantarki dan kansa, ta hanyar amfani da shara.

Hotunan kirkirar da ya yi mai kayatarwa sun dauki hankulan mutane a shafukan sada zumunta.

Wani dan Najeriya mai hazaka ya gina bandaki da ke samar da iskar gas na girki da wutar lantarki da kansa. Bekwarra Blog, wanda ya wallafa labarin a shafin impressive news a dandalin Facebook na Rant HQ Extention, ya bayyana cewa wannan fasahar tana da sauki kuma ta fi dadewa.

Hotunan mutumin yayin da ya ke gina bandakin kuma yana amfani da shi ya dauki hankulan masu amfani da dandalin sada zumunta.

Wasu daga cikin abubuwan da masu amfani da soshiyal midiya suka ce Dickson ya ce: “Abin takaici ne ganin yan Najeriya da dama sun san fasahar sarrafa makamashi na biogas musamman wadanda suka karanci physics da chemistry a makarantu. “Mai zai hana su dage su yi wani abu kan hakan su cece mu daga tsadar kudin gas.”Yanzu idan zaka cika tukunyar gas mai girman 12.5kg sai ka kashe N9500. Kuma galibi baya kai wata guda. Gaskiya muna bukatar mafita daga wannan rayuwa mai wahala.

” John Aduku ya ce: “Makamashi wanda kai iya narkewa a kasa. Ba sabon abu bane, tafi kasashen Afirka ta Gabas ka ga yadda fiye da kashi 50 na kasar ke amfani da shi. “Ya kamata karkara a Najeriya su rungume shi.

” Maryqueen Osita Blessing ta ce: “Eh, an kowa mana a makaranta a darashin biotechnology… a tsangayar genetics and biotechnology a Unical.”

Chinenyenwa Chigbu Eno ta ce: “Takwara ta mace ta gina irin wannan biogas din, amma nata na amfani da kashin kaji don samar da gas din girki.” Mavis Marvelous Mavis ya ce: “Yanzu wato idan ba ka yi bayan gida ba girki kenan.”

Related Articles

Back to top button