LabaraiSiyasa

EFCC Ta Ayyana Neman Dan Takarar Sanatan APC A Kano, A.A Zaura Ruwa-a-jallo

Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta’annuti, EFCC ta bayyana neman dan takarar Sanatan Kano ta tsakiya a jam’iyyar APC, AbdulKareem AbdulSalam Zaura wanda aka fi sani da A.A Zaura.

Lauyan hukumar EFCC, Ahmad Rogha ne ya bayyana hakan ga manema labarai a ranar Litinin bayan da aka dawo da batun shari’ar dala miliyan 1.3 da ake yi wa A.A Zaura a babbar kotun tarayya da ke Kano.

Duk da cewa shari’ar da aka shirya yi wa dan siyasar ba ta samu ba, saboda rashin halartar alkalin da ke sauraron shari’ar, wanda aka ce yana halartar wani taron kasa a wajen birnin na Kano.

Amma duk da rashin samun halartar mai shari’ar, lauyan na EFCC ya bayyana cewa ya kamata A.A Zaura ya kai kansa ga hukumar. Kamar yadda BBC Hausa ta bayyana.

“Muna neman Zaura kuma za mu kama shi da zarar mun same shi”.

”A ƙa’ida, ya kamata a ce yana hannunmu domin kuwa kotu ta tabbatar da haka, amma ina tabbatar da cewa za a kama shi tare da gurfanar da shi a gaban kotu a zamanta na gaba ranar 30 ga Janairun 2023”.

Related Articles

Back to top button
error: Content is protected !!