LabaraiSiyasa

Gaskiya Ta Fito: Jami’ar FUD Ta Yi Magana Kan Kama Dalibin da Ya Taba Aisha Buhari

Gaskiya Ta Fito: Jami'ar FUD Ta Yi Magana Kan Kama Dalibin da Ya Taba Aisha Buhari

Hukumar jami’ar Dutse dake babban birnin jihar Jigawa ta tabbatar da kama ɗalibinta, Aminu Adamu, kan taɓa Aisha Buhari .

A wata sanarwa da hukumar FUD ta fitar ranar Litinin, tace ta tuntubi iyayensa kan lamarin kuma sun faɗi matakin da suka ɗauka.

Rundunar yan sanda a jihar Jigawa tace ko kaɗan bata da masaniya kan kama ɗalibin FUD.

Jigawa – Hukumar Jami’ar Dutse (FUD) jihar Jigawa ta tabbatar da labarin kama ɗaya daga cikin ɗalibanta, Aminu Adamu, bayan kalaman da ya yi kan uwar gidan shugaban ƙasa, Aisha Buhari. A ranar 9 ga watan Nuwamba, 2022, Dalibin ya sanya Hoton Aisha Buhari a shafinsa na Tuwita kana ya rubuta, “Su mama anci kudin talakawa an ƙoshi.”

Mai magana da yawun jami’ar FUD, Abdullahi Bello, yace lokacin da lamarin ya faru makaranta na cikin Hotu saboda haka baya karkashin kulawar makaranta sa’ilin da ya yi rubutun.

“Lamarin mara daɗi da ya rutsa za Aminu Adamu ya faru ne lokacin muna hutu. Ya yi rubutun a Tuwita a karan kansa na Aminu ba a matsayin ɗalibin FUD ba.

Sun bi diddiginsa har Dutse suka cafke shi.” “Hukumar makaranta ta tuntuɓi iyayensa waɗanda har sun ɗauki Lauyan da zai kare shi kuma suna fatan warware matsalar cikin sauki.

” Arewa Top ta gano cewa ɗalibin ya fito ne daga garin Azare jihar Bauchi kuma yana shekarar ƙarshe a Kwas din Enviromental Management a jami’ar.

Rahotanni sun ce jami’an tsaron farin kaya SSS ne suka damƙe shi, kuma tun wannan lokacin basu ce uffan ba duk da sukar da ‘yan Najeriya ke yi.

A halin yanzun, hukumar yan sanda reshen jihar Jigawa tace bata da masaniya kan batun kama ɗalibin. Kakakin hukumar, Lawam Adam, yace duk wani kame da dakarun ‘yan sanda zasu yi a sassan jihar Jigawa wajibi ne a sanar da Hedkwata kafin aiwatarwa. Yace game da wannan lamarin kam har yanzun babu wanda ya sanar da hukumar kama ɗalibin a ciki ko wajen Jigawa, kamar yadda Punch ta rahoto.

“Don Allah Ku Yafe Wa Ɗanmu”, Iyayen Aminu Azare Sun Roki Aisha Buhari Ta Yi Masa Afuwa.

A wani labarin kuma Iyayen ɗalibin da ya taba kimar Aisha Buhari a Tuwita sun roki Uwar gidan Shugaban kasa ta masa Afuwa Iyaye da yan uwan Aminu Azare, dalibin jami’ar FUD da jami’an tsaro suka kama kan zargin ‘zagin’ Aisha Buhari sun roki matar shugaban kasar ta yafe wa dansu ta sake shi.

Shehu Baba-Azare, kawun Aminu ya ce ba su san an kama shi ba bayan kwana biyar da faruwar abin lokacin da abokin karatunsa ya musu waya cewa bai san inda ya ke ba.

 

Related Articles

Back to top button