Labarai

Gwamna El-Rufai Ya Rantsar Da Sarkin Jere Na 11

Gwamna El-Rufai Ya Rantsar Da Sarkin Jere Na 11

Gwamna El-Rufai Ya Rantsar Da Sarkin Jere Na 11

Gwamna El-Rufai Ya Rantsar Da Sarkin Jere Na 11

A yau Juma’a ne Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmed El-Rufa’i ya rantsar da sabon Sarkin Jere na 11, Alhaji Abdullahi Daniya a wani gagarumin bikin da aka gudanar a babban filin ƙwallon ƙafa na garin Jere.

Bikin wanda ya gudana cikin tsattsauran tsaro, ya samu halartar mataimakiyar gwamnan, Hajiya Hadiza Balarabe da kusan ɗaukacin ‘yan majalisar zartaswa na Jihar Kaduna, da mai martaba Sarkin Zazzau, Alhaji Ahmed Nuhu Bamalli, da Jakadan Nijeriya a Ƙasar Benin, Janar Yusuf Tukur Buratai mai ritaya da Shugaban Hukumar Kula da Shige da Fice ta Ƙasa, Isah Jere Idris da sauran manyan baƙi daga ko ina a sassan ƙasar nan.

Da yake jawabi bayan rantsarwar, Gwamna El-Rufai ya jaddada muhimmancin zaman lafiya a tsakanin al’umma wanda ya ce shi ne babban ginshiƙin kawo ci gaba mai ma’ana. Ya yaba wa al’ummar Jere bisa yadda suka rungumi zaman lafiya tare da yin jaje ga waɗanda ɓarnar ‘yan bindiga ta shafa.

Ya ƙara da cewa, gwamnati na ci gaba da yin duk abin da za ta iya wajen tabbatar da tsaro a faɗin Jihar Kaduna, kana ya nemi a ƙara bai wa jami’an tsaro haɗin kai domin su ji daɗin ɗorewa da ƙwazon da suke nunawa a yanzu haka wajen fatattakar ‘yan ta’addar.

Hoto na gabadaya

Wakazalika, Gwamna El-Rufai ya yi tsokaci a kan matakan da gwamnatinsa take ci gaba da ɗaukawa wajen kare martabar sarakuna da ɗaga darajojinsu a Jihar Kaduna, inda ya yi nuna da cewa an raba wa Hakimai motoci kuma a yanzu haka gwamnatin na shirin sake raba wasu motoci 88 duk dai ga sarakuna a jihar.

Ya yi kira ga al’ummar Jere su martaba sabon sarkin nasu da ba shi haɗin kai don ya ji daɗin sauke nauyin da aka ɗora masa na jama’a. Daga nan ya yi addu’ar Allah ya gafarta wa Sarkin Jere na 10, Dakta Sa’ad Usman.

Shi ma da yake jawabi, Shugaban Ƙaramar Hukumar Kagarko, Honarabul Auzara Rabo, ya gode wa Gwamna El-Rufai bisa bisa gagarumin ci gaban da ya kawo yankin ƙaramar hukumar da bai wa matasa dama a dama da su a fagen siyasa wanda ya ce hakan ne ya sa aka samu matashi a karon farko da ke shugabantar ƙaramar hukumar.

A nasa jawabin, mai martaba Sarkin Jere, Alhaji Abdullahi Daniya, ya gode wa dukkan jama’ar da suka halarci bikin, sannan ya jaddada ƙudirinsa na ƙara haɗa kan al’umma da tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin masarautar.

Daga bisani, Sarkin Jere ya naɗa Gwamna El-Rufai sarautar Sarkin Yaƙin Jere tare da miƙa masa malafa, da sandar kiwo da kuma ƙaton bajimin sa domin kiwo.

Related Articles

Back to top button
error: Content is protected !!