Labarai

Gwamnatin Birtaniya Ta Gayyaci Malaman Najeriya Aiki, Za Ta Biya Albashi Mai Tsoka Na Miliyoyin Naira

Gwamnatin kasar Birtaniya na yi wa malaman Najeriya tayin albashin Naira miliyan 15 duk shekara.

Wata sanarwa da aka fitar a shafin gwamnatin na Birtaniya ta ce malaman da suka cika sharudan suna iya neman aikin

Kasashen da aka ce za su iya neman aikin sun hada da Najeriya, Ghana, Singapore, Afirka ta Kudu, Hong Kong da sauransu.

Daga watan Fabrairun shekarar 2023, malaman Najeriya da suka yi hijira zuwa Birtaniya za su rika samun albashin N15.065 miliyan duk shekara.

Bayanai daga shafin intanet na gwamnatin Birtaniya ya bada sharuda da dokoki ga mutanen da ba yan Birtaniya ba amma ke da sha’awar koyarwa a kasar, ya ce albashi zai danganta da cancanta da kuma kasar da malamin ya fito.

Jerin kasashen da aka amince su nemi aikin

A cewar rahoton, Birtaniya, a farkon watan Disamba ta ambaci Najeriya cikin jerin kasashen Afirka wadanda yan kasar za su iya neman biza na koyarwa ta hukumar kula da koyarwa a Birtaniya, daga Fabrairun 2023.

Sauran kasashen sun hada da Ghana, Hong Kong, Indiya, Jamaica, Singapore, Afirka ta Kudu, Ukraine da Zimbabwe.

The Punch ta rahoto cewa wadanda za su nemi aikin ba su bukatar kwarewa na koyarwa domin kasar za ta bada horaswa ga masu sha’awar yin hijira zuwa can.

Daga bayanai a kasar Birtaniya, dukkan malaman da suka cancanta za a rika biyansu a kalla fam 28,000 ko fiye da hakan idan suna aiki a Landan.

Related Articles

Back to top button