LabaraiSiyasa

Gwamnatin Kano Ta Janye Dokar Hana Adaidaita Sahu Bin Manyan Titunan Jihar

Gwamnatin Kano Ta Janye Dokar Hana Adaidaita Sahu Bin Manyan Titunan Jihar

Gwamnatin Jihar Kano, ta bayyana cewar ta janye dokar da ta kafa na hana baburan Adaidaita Sahu bin wasu manyan titunan jihar.

Wannan na dauke ne cikin wata sanarwa da shugaban hukumar KAROTA, Baffa Babba DanAgundi, ya fitar a yau Alhamis.

Tun da fari, gwamnatin Kano, ta ce ta sanya dokar ne don kawo gyara a harkar sufuri a jihar.

Wasu daga cikin titunan da aka hana baburan Adaidaita Sahu sun hadar da titin Tal’udu zuwa Gwarzo, titin Hadeja zuwa Gezawa, titin Ahmadu Bello, titin gidan gwamnatin jihar da sauransu.

Wannan lamari ya janyo rudani da maganganu na bacin rai a tsakanin mutane musamman masu amfani da ababen hawa na Adaidaita Sahu.

Sai dai gwamnatin ta yi nazari kam janye dokar har zuwa nan da wani lokaci biyo bayan kiranye-kiranyen jama’a.

Related Articles

Back to top button