Gwamnatin Tarayya Ta Raba Kayan Sarrafa Madarar Shanu A Jihar Kano
Gwamnatin Tarayya Ta Raba Kayan Sarrafa Madarar Shanu A Jihar Kano
Gwamnatin Tarayya Ta Raba Kayan Sarrafa Madarar Shanu A Jihar Kano

Ma’aikatar aikin gona da raya karkara ta raba sabbin motocin raba madarar shanu mai na’urorin sanyi, guda 100 ga kungiyar masu sayar da madarar, da ke jihar Kano.
Darakta a ma’aikatar aikin noma da raya karkara da ke jihar Kano, Alhaji Baba Gana ne ya mika kayan ga kungiyar a madadin ma’aikatar.
Alhaji Gana ya ce, sauran kayan da aka raba wa kungiyar sun hada da janareta mai karfin 20KBA. Sannan gwamnatin tarayya ta dauki wannan matakin na raba Kayan domin tabbatar da kara tsaftace kasuwancin na madara a jihar da kuma a kasa baki daya. A cewarsa, gwamnatin tarayya ta yi namijin kokari wajen ganin ana kara bunkasa fannin na sarrafa madara a kasar nan.
Gwamnatin tarayya ta dauki wannan matakin na raba Kayan domin tabbatar da kara tsaftace kasuwancin sayar da nadarar a jihar da kasa baki daya.
Alhaji Gana ya ci gaba da cewa, an kuma gina cibiyoyin biyu na tara madarar shanu, inda aka mika su ga kungiyar.
Daraktan ya bayyana cewa, an kuma horas da wasu daga cikin ‘ya’yan kungiyar kan fanni daban-daban na hada-hadar kasuwancin madarar ta shanu.