Hukumar NAFDAC Tace Zata Sanya Kafar Wando Daya Da Wanda ke Shigo Da Man Bilicin Ba Bisa Ka’ida Ba
Hukumar NAFDAC Tace Zata Sanya Kafar Wando Daya Da Wanda ke Shigo Da Man Bilicin Ba Bisa Ka'ida Ba
Hukumar NAFDAC Tace Zata Sanya Kafar Wando Daya Da Wanda ke Shigo Da Man Bilicin Ba Bisa Ka’ida Ba

A wani bincike da kafar labarai ta tayi, an gano Nigeria na cikinkasashen da aka fi amfani da man bilicin.
Yan mata kan canja launin fatarsu daga baki zuwa fari dan ganin sun burge maza ko kuma abokan huldarsu.
A wani bincike da masana lafiya sukai, sun tabbatar da yadda man bilicin ke ragewa fata karfi da kuma barazana a gareta.
Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa (NAFDAC) ta ce za ta kawar da kasuwanni da shaguna da masu shigo da da man bilicin wanda ba’a amince da shi ba.
Hukumar ta ce za ta fara aiwatar da aikin ne a shagunan kayan kwalliya da kuma shagunan da ake sarrafa irin mayukan wanda basu samu sahalewar hukumar ba.
Hukumar na bayyana wannan batun ne a wani taron bita da hukumar ta shirya, tare da hadin gwiwar kungiyar ‘yan jaridun lafiya ta Najeriya (ANHEJ).
A rahotan da jaridar The Nation ta wallafa tace mukaddashin Darakta Janar ta hukumar, Dr. Monica Eimunjeze, ta ce:
“Za mu ci gaba da aiwatar da cikakken aiki. a dan haka Muna sanar da’yan Najeriya cewa zamu fara aiwatarwa da wani aiki a shagunan kayan kwalliya saboda yawanci anan ne aka fi samun mayukan, sannan a wasu shagunan ne ake sarrafa mayukan ba bisa ka’ida ba.
“Muna sane da mayukan da ke sahalewar doka. Amma abin da muke magana akai shine waɗan da basu da waccar sahalewar. Sabida haka muke son daukar matakin akan lamarin.