Labarai

In Gwamnati Ta Yi Mana Dam A Hunkuyi Za Mu Wadata Nijeriya Da Dankalin Turawa -Umaru Dikko

In Gwamnati Ta Yi Mana Dam A Hunkuyi Za Mu Wadata Nijeriya Da Dankalin Turawa -Umaru Dikko

In Gwamnati Ta Yi Mana Dam A Hunkuyi  Za Mu Wadata Nijeriya Da Dankalin Turawa -Umaru Dikko

In Gwamnati Ta Yi Mana Dam A Hunkuyi Za Mu Wadata Nijeriya Da Dankalin Turawa -Umaru Dikko

Masu karatunmu a wannan shafi na noma wanda masu iya magana kan ce, tushen arziki, makon, Wakilinmu Sabo Ahmad Kafin-Maiyaki ya yi tattaki, zuwa wata gona da ke garin Hunkuyi, karamar hukumar Kudan jihar Kaduna, inda ya tattauna da wani shaharren manomin rani, mai suna Alhaji Umaru Dikko wanda a tattaunawar ta su, ya bayyana, bukatar da masu noman rani a wannan yanki ke da ita, wadda za ta taimake su wajen bunkasa noman nasu domin wadata kasa da abinci da samar da aikin yi ga dimbin matasa.

Ga dai yadda tattaunawar ta mu ta gudana, a gonar ta sa da ke garin Hunkuyi, ranar Lahadin da ta gabata

Masu Karatunmu Za Su So Ka Gabatar Da Kanka.

Sunanan Alhaji Umaru Dikkon, ina zaune a cikin garin Hunkuyi, ni manomi ne, musamman na fi bayar da karfi a noman rani, wanda kamar yadda kake gani a halin yanzu a wannan gona tawa, wadda take a nan garib Hunkuyi.

Me Da Me Kake Noma wa A Wannan Gona Taka?

Ina noma kabeji, amma, babban abin da na fi noma was hi ne, dankalin Turawa.

Daga Ina Kuke Samun Wannan Irin?

Muna samun wannan irin ne daga Jos, amma saboda yanayin kyan kasarmu, har na mu a wasu lokutan yakan fi na Jos din kyau.

Iri Nawa Ne Nau’ukan Dankalin Da Kuke Dasa Wa?

A kalla muna noma dankali nau’in kola da daimon, wadanda dukkan wadannan nau’in dankalin suna yin girma a wannan kasa ta mu, har ma wasu wadanda ban ambata ba.

Shin Wai Shi Dankali Ya Ake Shuka Shi Ne?

Ita kwayar dankalin ake yanka wa sai a dasa a kasa daga nan zai kama sai ya ci gaba da rayuwa, sannan sai a yimasa noma daga nan sai in ya yi a hake shi.

Wane Lokaci Ne Ake Fara Dasa Shi?

Da zara ruwan sama ya dauke ne ake fara dasa shi, a cikin shekara daya mukan dasa shi sau biyu, yanzu haka ma bayan na ranin har zan damina muna yi, muna amfani da takin zamani na NPK 15-15-15 da kuma Uriya, amma kuma wanda ya yi amfani da takin gida sai ya fi samun amfani mai yawa.

Yaya Batun Kasuwar Dankalin?

Babbar matsalar da muke fama da ita, ita ce, yadda za nu adana shi, saboda haka da zarar ya zo dole, mu dayar da shi, duk yadda ta kama.

Wane Kira Kake Da shi Ga Gwamnati?

Kirana na farko shi ne, ta samar mana da kasuwa sai abu na biyu gwamnati ta samar mana da takin zamani abu na uku kuma shi ne gwamnati ta samar mana da dam, wanda za mu yi amfani da shi domin yin ban-ruwa sannan kuma karshe, idan muka samu wannan, noman dankalin Turawa da ma sauran nau’ukan amfani zai habaka a wannanan yanki.

Related Articles

Back to top button
error: Content is protected !!