Majalisar wakilan tarayya ta nuna takaicinta da rashin ganin Ministan jin kai duk da gayyatar da aka aike mata.
Shugaban kwamitin kasafi, Muktar Betara, ya nemi ministar, Sadiya Farouk, ta Sauka idan bata shirya gudanar da aikinta ba.
Ana ta kai ruwa rana tsakanin majalisar da Ministocin Kudi da jin kai kan wasu kuɗi da aka cusa a Kasafin kuɗin 2023 DUBA NAN: Danna “See First” karkashin.
Muktar Betara, shugaban kwamitin kasafi shi ne ya faɗi haka yayin zaman bincike kan kutsa biliyan N206bn a kasafin kuɗin 2023 daga ma’aikatar jin ƙai da walwala.
Hukumar dillancin labarai ta ƙasa (NAN) ta rahoto cewa ma’aikatar ta ware wa aikin raba ragar sauro Biliyan N206,242,395,000 kuma Bankin duniya ne ke ɗaukar nauyin shirin.
Shugaban kwamitin, Hon. Betara, wanda ya nuna fushinsa a fili ya kalubalanci cewa meyasa Ministar ta gaza zuwa ta kare sanya kuɗin, inda ya kara da cewa idan bata shirya ba ta aje aiki. “Duk lokacin da Kwamiti ya gayyaci ministar ba ta zuwa. Idan bata shirya aiki ba ya kamata ta sauka kawai,” inji Betara.
Daga ina aka samu matsalar tun farko? Da take bayanin inda aka samu kuskuren tun farko, Minista kudi, Hajiya Zainab Ahmed, tace an cusa abun ne tun a Ofishin Kasafi. Tace ya kamafa ace Ministan jin ƙai ta ankarar da Ofishin kamar yadda takwarorinta suka yi. Zainab Ahmed tace ma’aikatar tsaro, ma’aikatar makamashi da sauran ma’aikatun gwamnatin tarayya duk sun tafka kuskure amma suka garzaya aka gyara, kamar yadda The Cable ta ruwaito.