LabaraiSiyasa

Kirisimeti: Gwamnatin Bauchi Ta Raba Kayan Abincin Miliyan 145 Ga Kiristoci

Kirisimeti: Gwamnatin Bauchi Ta Raba Kayan Abincin Miliyan 145 Ga Kiristoci

Kirisimeti: Gwamnatin Bauchi Ta Raba Kayan Abincin Miliyan 145 Ga Kiristoci

Yadda gwamnatin bauchi ta raba kayan abincin ga kiristoci domin murnar kirismeti

Gwamnatin Jihar Bauchi ta raba shanu, raguna da kuma kayan abinci na sama da Naira miliyan 145 ga kiristoci da ke jihar don gudanar da shagulan bikin Kirisimeti cikin annashuwa da walwala.

Shugaban kwamitin rabon kayan kuma mai bai wa gwamnan jihar shawara kan harkokin ma’aikata, Mista Abdon Dalla Gin, ne ya shaida hakan ga manema labarai yayin kaddamar da rabon a ranar Juma’a.

Ya ce, “Wannan tallafi da gwamnati ta ke bayarwa ga al’ummar kirista lokacin bukukuwa ba farau ba ne, abu ne da ta saba a kowace shekara domin kyautata wa al’ummarta don su kasance cikin walwala yayin bukukuwa.”

Abdon ya yaba wa gwamna Bala Muhammad bisa wannan karamci tare da yin adalci wa kowane bangare na al’ummar jihar.

Haka nan shugaban kwamitin ya ce sun yi tsari mai kyau yayin rabon ta yadda dukkan bangarorin kungiyoyi da majami’u da suke jihar za su amfana da tallafin ba tare da nuna wariya ga kowane bangare ba

Kana ya ba da tabbacin cewa kiristocin Jihar Bauchi za su ci gaba da mara wa gwamnatin wajen ganin sun ci gaba da cin gajiyar romon Dimokaradiyya.

Wasu daga cikin wakilan kungiyoyi da Majami’u da suka karbi tallafin sun yi godiya ga gwamnan jihar, bisa tallafa musu da yake don samun sauki wajen gudanar da bukukuwan kirsimeti kowace shekara.

Related Articles

Back to top button