Labarai

Ko Gezau Babu Abun Da Ke Firgita Takarata Ta Gwamnan Gombe – Inuwa

Ko Gezau Babu Abun Da Ke Firgita Takarata Ta Gwamnan Gombe – Inuwa

Ko Gezau Babu Abun Da Ke Firgita Takarata Ta Gwamnan Gombe – Inuwa

Ko Gezau Babu Abun Da Ke Firgita Takarata Ta Gwamnan Gombe – Inuwa

Gwamnan Jihar Gombe kuma dan takarar Gwamna na jam’iyyar APC a zaben 2023, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya shaida cewar babu wani abun da ke firgita shi dangane da takarar kujerar gwamnan Jihar don haka shi kam ‘Ko-Gezau’

Inuwa ya yi ikirarin cewa abokan hamayyarsa ba su wani tada masa hankali kuma ba su zama masa barazana kan neman tazarce da ya ke yi ba, domin ya san kwaf daya zai musu ya zarce lura da abun da ya kira gamsuwa da salon mulkinsa da al’ummar Gombe suka yi sakamakon kyawawan ayyukan da ya shimfida musu a zangonsa na farko.

Gwamnan ya ce ya gudanar da ayyukan raya birane da karkara a gundumomi 114 da suke fadin jihar kuma har yanzu yana da cikakken tasiri a zukatan masu zabe wannan dalilin ne ya sanya ya ce shi kam ‘ko-gezau’ ba wata jam’iyya ko dan takarar da za ta firgita shi ko zama masa damuwa balle barazana.

 

“Kun gani da kanku ai, kun ga yadda dumbin jama’a ke fitowa matasa da dattawa, mazansu da mata. Dukka domin su nuna soyayya da goyon baya ga jam’iyyar APC bisa kwarin guiwar da suke da shi na cewa APC za ta iya don sun gani a kasa.

 

“Ina da cikakken kwarin guiwa da tabbacin za mu ci zabe. Me zai sanya na ji gezau? Ina da goyon bayan jama’a.”

 

A kauyen Todi, gwamnan ya yi alkawarin gina musu masallaci da coci kamar yadda al’ummar yankin suka roka. Sannan kuma zai gina hanya, makarantu da gadoji Billiri ta arewa.

Related Articles

Back to top button