Labarai

Kwana Hudu da Aure, Amarya Ta Kama Angonta da Yar Uwarta Suna Jin Dadi a Gado

Kwana Hudu da Aure, Amarya Ta Kama Angonta da Yar Uwarta Suna Jin Dadi a Gado

Kwana hudu bayan ɗaura musu Aure, wata amarya ta kama Angonta yana saduwa da ‘yar uwarta a kan gado.

Sabuwar amaryar da abun ya sosa wa zuciya, tace lamarin ya taɓa ta yadda ta koma Otal na tsawon mako ɗaya ba wanka da yawo.

Ta garkame lambobin mahaifiyarta da Surukarta saboda sun nemi ta yafe wa mijin da yar uwarta.

Wata mata ta ja hankalin ma’abota shafukan sada zumunta bayan ta tona yadda ta kama Mijinta na holewarsa a gado tare da ‘yar uwarta kwanaki huɗu da ɗaura musu aure.

A wani Bidiyo da ta saki a shafin TikTok, Matar tace abinda ta gani wanda bata taɓa tsammani ba ya fasa mata zuciya ta yadda ta killace kanta a dakin Otal tsawon mako ɗaya, ba wanka ba yawo.

Yayin da ta koma wurin aiki, ta ci karo da Angonta da kuma ‘yar uwarta sun zo neman ta yafe musu. Daga baya ta tsoshe lambobinsu.

Ba zata yafe musu ba

Matar ta ƙara da cewa ta toshe lambar mahaifiyarta da kuma lambar Surukarta saboda sun roki ta yafe wa mutanen biyu.

Tace daga baya ta tattara kayanta ta koma gidan kawarta. Tace ba mamaki shiyasa ‘yar uwarta ta yi shigar fararen kaya a ranar bikin. A wasu kalamansa, amaryar tace: “Na shiga yanayi na koma Hotel ba wanka ba yawo na tsawon mako guda.

Ranar da na fita aiki dukkansu sun zo neman gafarata. Na tambaye su anya ɗan uwan mijina ne uban yaron nan ɗan shekaru hudu, suka fara inda-inda.” “Na toshe lambobinsu baki ɗaya har da mahaifanmu saboda sun roki na yafe musu. Daga nan na koma gidan hutun ƙawata na kama holewa ta da masoya da zuwa wurare daban-daban.”

Yadda mutane suka faɗi ra’ayoyinsu

user7673479997905: “Aikin da kike ne ya cece ki daga shiga matsanancin hali, yar uwarki ta wuce gona da iri, ina miki fatan warwarewa wata rana.”

” Fun in the bakes yace: “Ka ci amanata ni kuma na datse alakarmu, ba zan ji tsoron faɗin gaskiya ba. Amma daga karshe zai girbi abinda ya shuka, ni kuma na yi gaba.”

Related Articles

Back to top button