Labarai

Manoman Alkama Sun Koka A Kan Rashin Samun Iri

Manoman Alkama Sun Koka A Kan Rashin Samun Iri

Manoman Alkama Sun Koka A Kan Rashin Samun Iri

Manoman Alkama Sun Koka A Kan Rashin Samun Iri

A yayain da ake shirye-shiryen fara shukar alkama daga yanzu zuwa tsakiyar watan Dismba, manoman alkama a kasar nan, sun koka kan rashin samun iri.

A duk watan Dimsambar kowace shekara ce, manoman ke fara shirye-shiryen shukar alkamar, inda suka yi nuni da cewa, matsalar za ta iya shafar burin da suke da shi na samun amfani mai yawa, inda kuma hakan, zai kara janyo a samu wawagegen gibi na bukatar da ake da ita ta alkamar a kasar nan da ta kai fiye da tan miliayn 4.1.

Wasu daga cikin maoman alkamar da aka tattauna da su a jihar Katsina sun bayyana cewa, duk da irin tsadar farashin takin zamani don yin noman na alkamar, sun nuna aniyarsu ta fara shukar alkamar a kan lokaci, domin su cike gibin da suka samu bara.

Daya daga cikin manoman na alkamar a jihar Katsaina Malam Murtala Mairuwa, ya koka kan rashin tallafin da manoman alkamar ba sa samu daga gwamnati, inda ya yi nuni da cewa, koda za su samu tallafin daga gun gwamnatin, ya an zuwa ne a makare.

Sai dai, Mairuwa, ya ci gaba da cewa, kakar alkama a shekarar da ta wuce, gwamnatin ta samar wa da manoman dauki ta hanyar babban bankin Nijeriya CBN, musamman ta hanyar samar da takin zamani da sauran kayan aikin alkamar.

A cewarsa, kamata ya yi a fara shuka Alkamar akalla daga cikin watan Nuwamba, inda hakan zai baiwa manomin ta damar samun yin girbin ta da dama, inda ya kara da cewa, ko a shekarar da ta wuce, an rabawar da manomanta da kayan aikin ne a cikin watan Disamba.

Mairuwa ya kara da cewa, wata matsalar da manoman ta ke fuskanta shine yadda ake samun wasu marsa kishi kuma wadanda suka kasance ba manonta ba, ke dakile zuwan daukin na gwamnatin ga ainahin manoman da ke yin nomanta.

Har ila yau, a cikin karamar hukumar Bakori da ke a cikin jihar Katsina, akasarin manomanta sun dogara ne akan samun ruwa daga kogin Jare domin yin noman ranin ta, inda daya daga cikin manoman nata Abdurrahman Kabir ya sanar da cewa, a kakar noman ta a wannan shekarra, ba a samu yawan ruwan sama da ake bukata ba

A cewar Kabir, manoman na alkamar a wannan shekarar, na fusntar kalubalen tsadar farashin kayan aikin na Alkamar, musamman idan aka yi la’akari da kudaden da suke kashewa wajen sayen man fetur domin yin ban ruwa.

An ce yanzu haka, farshin buhu day na alkamar mai nauyin kilo 100, ana sayar da shi kan naira 48,500 a kasuwar ta Bakori, inda kuma wasu sun ce, farshin ya kai sama da naira 50,000.

Har ila yau, a jihar Kano kuwa an ce, tuni wasu manoman alkamar suka fara koma wa gona domin fara yin aiki gadn-gadan, amma sai dai, abin takaici har yanzu ba su iya samun iri ba da kuma samun sauran dauki a fannin.

Biyo bayan wani bincike da aka gudanar sama da shekarun da suka wuce, alkasrin namoman na Alkamar sun fi dogara ne da samun Irin daga gun kafanonin da ke samar da irin domin sayawar da manoman.

A cewar wasu daga cikin manoman, tun lokacin da hukumar gudanar da bincike aikin noma da ke tabkin Chadi ta dakatar da raba da ingantaccen irin, an bar manoman da fafutukar nemo irin da ya dace.

Wani manominta a jihar Kano Alhaji Surajo Bello ya bayyana cewa, duk da karancin da ake fuskanta na alkamar a fadin duniya, a wannan shekarar, ba su samu daukin gwamnatin tarayya ta hanyar shirin noma na Anchor Borrower ba.

Ya ce, abin takaice ne ganin cewa duk da an sa manoman na Alkamar a cikin jeren manoman da za su amfana da daukin na babban bankin Nijeriya CBN, amma ba sa samun daukin.

Shi ma wani manoman na alkamar, Alhaji Musa Mu’azu Garun Babba ya sanar da cewa, shekaru da dama da suka wuce, an bar manoman na alkamar ne kawai suna sayen irin daga gun kamfanin da ke samar da irin.

 

Related Articles

Back to top button
error: Content is protected !!