LabaraiSiyasa

Mataimakin Atiku, Tambuwal, Da Wasu Jiga-Jigan PDP Sun Lallaba Sun Gana da Obasanjo

Abokin takarar Atiku Abubakar, Gwamna Okowa na jihar Delta ya jagoranci jiga-jigan jamiyyar PDP sun sa labule da tsohon shugaban kasa Obasanjo.

Darakta janar na kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa a PDP, Gwamana Aminu Tambuwal na cikin wakilan da suka je Abeokuta ranar Asabar.

Ana hasashen dai wannan ziyara ba zata rasa alaka da rigingimun cikin gida da suka hana PDP zaman lafiya ba.

Ogun – Ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP, Gwamna Ifeanyi Okowa na jihar Delta ya jagoranci wakilan jam’iyyar sun sa labule da tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo, a Abeokuta ranar Asabar.

Sauran tawagar wakilan sun haɗa da Darakta Janar na kwamitin yakin neman zaɓen shugaban kasa a PDP, Gwamna Aminu Tambuwal na Sakkwato da tsohon gwamnan Jigawa, Sule Lamido.

Mai taimakawa tsohon shugaban kasa kan harkokin watsa labarai ne ya sanar da haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar sakamakon rashin sanin yan jarida gabanin fara taron.

A cewar sanarwa, taron wanda ya gudana a sirrance ya samu halartar tsohon gwamnan jihar Osun, Olagunsoye Oyintola, tsohon gwamnan jihar Kuros Riba, Liyel Imoke, da kuma d’an kasuwa, Oyewole Fasawe.

Related Articles

Back to top button