Labarai

Matsalolin Da Kirsimetin Bana Ke Fuskanta

Matsalolin Da Kirsimetin Bana Ke Fuskanta

Matsalolin Da Kirsimetin Bana Ke Fuskanta

Matsalolin Da Kirsimetin Bana Ke Fuskanta

Yayin da aka gab da shiga bukuwan kirsimeti da na sabuwar shekara wanda a irin wannan lokacin ya kamata a ce, mutane sun wadata da abinci, yadda za a gudanar da wadannan bukuwa cikin yalwa da taiamaka wa marasa karfi, amma sai ga shi, a wannan lokacin alamu na nuna cewa, hakan da kamar wuya, saboda tashin farashin gwauron zabon da kayan abincin ya yi.

Kayan abinci irin su shinkafa da mai da kaji da kayan miya da kayan kyale-kyale da ake ado da su a irin wannan lokaci domin nuna farin-ciki da annashuwa, yanzu haka wadannan kayan sun fi karfin talaka.

Sai dai, a binciken da aka yi a wasu manyan kasuwannin Binin, wato babban birnin jihar Edo, ya nuna cewa, hakan ta faru ne, saboda gwamnati ba ta sa idi kan yadda ‘yan kasuwa ke sayar da kayansu.

Farashin shinkafar gida da ta waje duk ya tashi. Misali, buhun shinkafa mai nauyin kilgiram 50 a kasuwar Oba a da ana sayar da ita naira 40, 000 amma yanzu ta koma naira dubu 50, 000.

Wata mata mai suna Mary-Jane Eche, da ke sana’ar kwalliya a uunguwar Upper Mission a Binin ta ce  farashin kayan abinci a kasuwanni ya yi tashin da ’yan Nijeriya da yawa ba za su iya saya ba.  Ta ce, farashin abinci ma fi sauki ga dan Nijeriya kamar shinkafa da makamantanta duk farashinsu ya tashi.

 

 

Related Articles

Back to top button