LabaraiSiyasa

Nuhu Ribadu ya Bayyana Matakin da Zai Dauka Kan Hukuncin Kotu

Nuhu Ribadu ya Bayyana Matakin da Zai Dauka Kan Hukuncin Kotu

Nuhu Ribadu ya Bayyana Matakin da Zai Dauka Kan Hukuncin Kotu

Nuhu Ribadu ya Bayyana Matakin da Zai Dauka Kan Hukuncin Kotu

Tsohon shugaban hukumar EFCC, Malam Nuhu Ribadu, yace bai amince da hukuncin kotun daukaka kara ba a zaben fidda gwani na takarar gwamnan jihar Adamawa.

Sai dai kuma, yace bayan tuntubar ‘yan uwa, abokan arziki da shugabannin siyasa na matakai daban-daban, ya yanke hukuncin kin daukaka karar.

Ya sanar da cewa wannan ne karo na biyu da ya nemi tikitin amma bai samu ba, kuma yayi hakan ne domin kishin jiharsa da neman damar kawo mata cigaba.

Nuhu Ribadu yace bashi da niyyar kalubalantar hukuncin kotun daukaka kara wacce ta jaddada Aishatu Binani matsayin ‘yar takarar kujerar gwamnan jihar Adamawa a jam’iyyar APC, jaridar Premium Times ta rahoto.

Binani sanata ce dake wakiltar Adamawa ta tsakiya kuma ta lallasa Nuhu Ribadu, tsohon shugaban hukumar EFCC da Jibril Bindow, tsohon gwamnan jihar inda ta lashe zaben fidda gwani da aka yi a ranar 26 na watan Mayu.

Ribadu ya kalubalanci sakamakon zaben a gaban babbar kotun tarayya dake jihar.

A hukuncin alkali Abdulaziz Anka, ya soke zaben fidda gwanin tare da bayyana cewa jam’iyyar bata da ‘dan takarar gwamna a APC a Adamawa.

Sai dai kotun daukaka karan a ranar 24 ga watan Nuwamba tayi fatali da hukuncin babbar kotun tare da jaddada Binani matsayin sahihiyar ‘yar takarar gwamnan.

 

Related Articles

Back to top button