Romon kunnen ƙudirin bai wa ɗalibai ramce, shiri ne da gwamnati ke yi na daina kula da jami’o’i ɗungurugum – ASUU
Romon kunnen ƙudirin bai wa ɗalibai ramce, shiri ne da gwamnati ke yi na daina kula da jami’o’i ɗungurugum – ASUU
Romon kunnen ƙudirin bai wa ɗalibai ramce, shiri ne da gwamnati ke yi na daina kula da jami’o’i ɗungurugum – ASUU

Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa (ASUU) ta zargi gwamnatin Najeriya ta na ƙoƙarin shigo da dabarar tsame hannayen ta daga ɗaukar nauyin jami’o’in tarayya, ta hanyar shigo da tsarin bai wa ɗalibai ramce.
An dai bijiro da ƙudirin neman a kafa dokar da gwamanti za ta riƙa bai wa ɗaliban jami’o’i ramce, kuma yanzu haka ƙudirin ya na Majalisar Tarayya, har ma Dattawa da Wakilai sun kammala karanta shi, sun miƙa shi kuma sun amince da shi. Abin da kawai ya rage a yanzu shi ne Shugaba Muhammadu Buhari ya sa masa hannu.
Tun cikin 2016 ne dai Ɗan Majalisar Tarayya daga Legas, wanda a yanzu shi ne Kakakin Majalisar Tarayya, Femi Gbajabiamila ya gabatar da ƙudirin.
Idan har Shugaba Muhammadu Buhari ya sa wa ƙudirin hannu ya zama doka, to gwamnatin tarayya za ta kafa Bankin Bunƙasa Ilmi, wanda zai riƙa bai wa ɗaliban jami’a ramce.
Sai dai kuma ASUU ta yi tir da wannan ƙudiri, ta ce ana so ne a shigo da tsarin da karatun jami’a zai gagari ɗan talaka.
Haka Shugaban ASUU Emmanual Osodeke ya bayyana a cikin wata sanarwar da ya fitar a ranar Talata, bayan tashin su daga taron Majalisar Zartaswar ASUU, wanda ya gudana a Jami’ar Calabar.
Ya ce sun ga ishara, domin duk sauran ƙasashen da su ka taɓa yin irin wannan tsari, bai yi alfanu ba, kuma su masu yi watsi da tsarin.
ASUU ta kuma yi tir da riƙe masu albashi da gwamnatin tarayya ta yi.