Labarai

Rugurugu: Kwamandan Boko Haram Ya Bayyana Gaskiyar Dalilin Da Yasa Shi Da Mayakansa Suka Mika Wuya

Rugurugu: Kwamandan Boko Haram Ya Bayyana Gaskiyar Dalilin Da Yasa Shi Da Mayakansa Suka Mika Wuya

Rugurugu: Kwamandan Boko Haram Ya Bayyana Gaskiyar Dalilin Da Yasa Shi Da Mayakansa Suka Mika Wuya

Mallam Adamu Rugurugu ya magantu a kan dalilin da yasa shi da mayakansa suka saduda sannan suka ajiye makaman yakinsu.

Tsohon kwamandan na kungiyar Boko Haram ya bayyana cewa ya zauna ya yi wa kansa wa’azin ta nutsu bayan ya gano cewa abun da yake aikatawa ba daidai bane.

Rugurugu wanda ya samo sunansa daga filin daaga ya kuma ce ya ajiye makamansa ne saboda Gwamna Babagana Zulum da ya shigo lamarin.

Borno – Wani kwamandan Boko Haram da ya mika wuya mai suna Mallam Adamu Rugurugu, ya bayyana dalilin da yasa ya ajiye makaman yakinsa.

Rugurugu ya bayyana cewa ya yanke shawarar fitowa daga jeji tare da mayakansa da dama saboda roko da shiga lamarin da Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno ya yi, jaridar Vanguard ta rahoto.

Rugurugu: Kwamandan Boko Haram

Ku tuna cewa dakarun soji sun kai zafafan hare-hare ta sama da kasa a wuraren mayakan Boko Haram da ISWAP lamarin da ya tursasa su ajiye makaman yakinsu da kuma mika wuya ga dakarun Operation Hadin Kai.

Na gano cewa abun da nake aikatawa ba daidai bane, Rugurugu

Da yake magana a sansanin da aka ajiye fiye da yan ta’adda 14,000 da suka mika wuya tare da iyalinsu a Maiduguri, Rugurugu ya ce ya samu sunansa ne daga ayyukansa a filin daaga yayin da suke arangama da dakarun gwamnati.

Sai dai kuma, ya bayyana cewa daga baya ya gano cewa abun da yake yi ba daidai bane kuma da gaske gwamnati take zata karbe su. Ya ce a dalilin haka ne ya yanke shawarar taimakawa wajen lallashin mayaka da dama kan su fito daga jeji sannan su mika wuya.

Kalamansa:

“Eh ina daga cikin kwamandojin. Na samu sunan Rugurufu wanda ke nufin babu tausayi daga filin daaga. A filin daaga ina da matukar hatsari saboda ina lalata duk abun da ya zo hanyata. Bani da tsoro. Wadannan makin da kuke gani a jikina ya kasancewa saboda rashin tsorona.

Gwamnan ya ji labarina sannan ya san cewa idan aka lallaba ni na fito, mayaka da dama zasu biyo ni kuma ta haka ne na fito na mika wuya. “A wannan sansanin, zan ce gwamnati da Janar Abdel Ishaq suna yiwa mu da muka mika wuya kokari sosai.

Sun lallashe ni sannan sun bani tabbacin cewa idan na ajiye wannan turba da bai da amfani, za a kula da mu. Za a kula da mata da yaranmu sosai. Idan waninsu ya shiga halin rashin lafiya, Muna da likitoci a nan da suke kula da su.

” Jaridar Vanguard ta tattaro cewa an fitar Rugurugu daga cikin jerin yan ta’adda masu taurin kai saboda nasarar da aka samu wajen tattaunawa da shi.

Haka kuma ya taimaka wajen lallashi mayaka da dama don su mika makamansu, yana mai basu tabbacin cewa da gaske gwamnatocin tarayya da jiha suke game da karbarsu.

A wani labarin, mun ji cewa rikicin manoma da makiyaya ya yi sanadiyar salwantan rayukan mutane takwas a jihar Borno.

Related Articles

Back to top button