Labarai

Shugaban Kasar Togo Ya Sallami Ministar Sojoji Da Hafsan Sojin Kasar

Shugaban Kasar Togo Ya Sallami Ministar Sojoji Da Hafsan Sojin Kasar

Shugaban Kasar Togo Ya Sallami Ministar Sojoji Da Hafsan Sojin Kasar

Shugaban Kasar Togo, Faure Gnassingbe, ya kori ministan sojojin kasar tare da nada sabon hafsan sojin kasar a kokarin yi wa gwamnatisa garanbawul.

Fadar shugaban kasar ta sanar da wannan matakin ne a ranar Alhamis, sai dai babu wani cikakken bayani kan garanbawul din, duba da kalubalen kungiyoyin da ke ikirarin jihadi kamar yadda sauran kasashen da ke Afrika ta Yamma ke fama da shi.

Tun daga watan Nuwamban 2021, Kasar Togo ta sha fama da hare-hare manya-manyan guda biyar da suka wakana a baya-bayan nan sun hada wanda mutum biyu suka mutu a Arewacin kasar da ke iyaka da Kasar Burkina Faso.

“An sauke Marguerite Essossimna Gnakade daga mukaminta na ministan sojoji,” a cewar sanarwar.

Bayan korar nata, ba a sauya ta da kowa ba, don haka rundunar sojin za ta ke amsar umarni ne kai tsaye daga fadar shugaban kasar.

Kanal Tassounti Djato, tsohon Hafsan Sojin Saman kasar, an yi masa karin girma zuwa Janar tare da nada shi a matsayin Hafsan Hafsoshin Sojojin kasar Togolese

Shi dai Djato, ya canji Janar Dadja Maganawe, wanda ke kan wannan mukami tun 2020.

Related Articles

Back to top button