Labarai

Sojoji Sun Kai Hari Sansanonin IPOB Sun Kwato Bama-Bamai Da Bindigu A Ebonyi Da Enugu

Dakarun runduna ta 82 tare da hadin gwiwar sojojin sama da ‘yan sandan Nijeriya da ma’aikatar tsaro ta cikin gida a ranar Litinin 19 ga watan Disamba 2022 sun kai wani samame na hadin gwiwa a sansanin IPOB/ESN da ke kauyen Amagu yankin Nkalaha da ke karamar hukumar Ishielu ta jihar Ebonyi.

A yayin farmakin, sojojin sun yi musayar wuta da ’yan kungiyar IPOB/ESN, inda hakan yasa aka samu nasarar kashe su da dama sauran kuma suka arce cikin dazuka da raunin bindiga.

Sojojin sun kwato zagaye 102 na kwabban alburusai mai nauyin 7.62mm da bindigogin famfo guda 2 da bindigu kirar gida guda 5 da kayan hada bam 27 da bama-bamai 24, da dai sauran kayayyakin shirin yaki.

A wani samame na dabam a wannan rana, sojojin da ke sintiri na yau da kullun a yankin Agubeji a jihar Enugu sun kama wani da ake zargi, Mista Martins Abogwu, da hada baki da kungiyar IPOB/ESN wajen kai hare-hare kan ‘yan kasa da ba su ji ba ba su gani ba.

Related Articles

Back to top button
error: Content is protected !!