Labarai
Wani Shahararren Dan Bindiga Ya Shiga Hannun ‘Yansanda A Jihar Kaduna
Wani Shahararren Dan Bindiga Ya Shiga Hannun ‘Yansanda A Jihar Kaduna
Wani Shahararren Dan Bindiga Ya Shiga Hannun ‘Yansanda A Jihar Kaduna

Rundunar ‘yan sandan Jihar Kaduna da ke ta kama wani shahararren dan bindiga da ke addabar mutanen jihar Bilyaminu Sa’idu a karamar hukumar Zariya.
Kakakin rundunar, DSP Mohammed Jalige, ya ce ‘yan sandan da ke aiki a yankin Tudun Wada Zariya ne suka kama dan bindigar yayin da suke samame a Kwarkwaron Manu yankin Basawa inda suka tare wasu mutum biyu a kan babur da ba shi da lamba.
Ya kara da cewa mutanen suna dauke da wasu jakunkuna da ake zargin an boye bindigogi.