Labarai

Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kai hari kan jami’an tsaro na Gwamna Okowa a Anambra, sun kashe uku

Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba da ke aiki a yankin Kudu-maso-Gabas sun sake kai wani hari a ranar Juma’a, inda suka kashe ‘yan sanda uku na sashen fashe-fashe, (EoD), rundunar ‘yan sandan jihar Delta, Asaba.

Wadanda aka kashen wadanda ke aiki a gidan gwamnatin jihar an kashe su ne a karamar hukumar Ihiala ta jihar Anambra.

‘Yan sandan na kan hanyarsu ta zuwa jihar Abia. Sun kasance tawagar gwamnan, wanda shine mataimakin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP.

An bayyana sunayen jami’an ‘yan sandan uku da suka mutu a matsayin Sufeto Lucky Aleh, Celestine Nwadiokwu da Jude Obuh.

Related Articles

Back to top button