Labarai
Wata Mata Ta Fashe Da Kuka Bayan Ta Binciko Wasu Hotuna a Jakar Makarantar Yarta Yar Shekaru 10, Bidiyon Ya Tada Hankulan Jama’a
Wata Mata Ta Fashe Da Kuka Bayan Ta Binciko Wasu Hotuna a Jakar Makarantar Yarta Yar Shekaru 10, Bidiyon Ya Tada Hankulan Jama'a
Wata mata ta aike da shafukan sada zumunta cikin rudani bayan ta bayyana abubuwan da ta gano a cikin jakar ‘yarta ta makaranta.
A cikin sakon TikTok, ta raba hotuna na bayanin soyayya da kuma hoton wani saurayi da ta samu daga jakar kuma ta ce zuciyarta ta karaya.
A cikin bayanin soyayya, marubucin ya bukaci ‘yarta ta san yana sonta kuma ya tambaye ta ko tana jin haka a gare shi? Shima masoyin ya ce tabbas tayi farin ciki sannan ya karasa da cewa yana sonta.
Hoton da aka makala na wani karamin yaro ne akan keke.