Labarai

Yadda Aka Kame Wani Matashi da Ke Ikrarin Shi Soja Ne, Ya Tafka Sata a Jihar Legas

Yadda Aka Kame Wani Matashi da Ke Ikrarin Shi Soja Ne, Ya Tafka Sata a Jihar Legas

Yadda Aka Kame Wani Matashi da Ke Ikrarin Shi Soja Ne, Ya Tafka Sata a Jihar Legas

Yadda Aka Kame Wani Matashi da Ke Ikrarin Shi Soja Ne, Ya Tafka Sata a Jihar Legas

Rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta kame wani matashi da ke ikrarin cewa shi jami’an sojan Najeriya ne.

An kama shi dauke kayayyaki daban-daban na sata, yanzu haka za a gurfanar dashi a gaban kotu.

Ana yawan samun ‘yan Najeriya da ke amfani da kakin soja wajen damfarar jama’a, musamman a kudu.

Wani mutum dan shekaru 39 mai suna Andy Edwards ya shiga hannun jami’an ‘yan sanda bisa zargin ikrarin shi kyaftin din soja ne a Legas, inda ya iakata fashi da makami. Mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda, Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da kama matashin a ranar Lahadi a wata sanarwa da ya fitar, Daily Nigerian ta ruwaito.

Hundeyin, ya shaida cewa, wanda aka kamen soja ne bogi, wanda ke fitowa a matsayin mai mai sana’ar talla. Kana yana gayyato ‘yan mata da sunan zai dauke su aiki kafin daga bisani ya sace motocinsu ko dan abinda suka zo dashi.

Ya ce an kwamushe Andy ne biyo bayan dogon bincike da jami’ai suka yi bayan da aka shigar da karar ya sace motar wata mata kirar Lexus RX330 SUV, rahoton Daily Sun.

A cewar Hundeyin:

“Bincike ya kai ga bankado wata mota kirar Ford Edge SUV mai lamba KRD 276 EG, keken dinke daya da na’urar POS daya mai dauke katunan SIM guda shida a gidan wanda ake zargin. “Haka nan kuma an kwace kakin kakin soja guda biyu da lambar mota guda – AFL 469 GD. “Yayin da ake ci gaba da bincike, ana kira ga mai mota kirar Ford SUV din da zo ya ba da bayani ya amshi kayarsa. Za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kuliya bayan kammala cikakken bincike.”

Hundeyin ya kuma tabbatar wa al’ummar jihar Legas ci gaba da jajircewar jami’an ‘yan sanda wajen wanzar da zaman lafiya da kare rayukan al’umma.

Related Articles

Back to top button