Labarai

Yadda wata matan aure ta kashe mijinta saboda ya ce zai yi mata kishiya

Yadda wata matan aure ta kashe mijinta saboda ya ce zai yi mata kishiya

Wata matar aure mai suna Salamatu Shehu ta yi ajalin mijinta mai suna Mallam Shehu a kauyen Rafin Gero da ke karamar hukumar Anka na Jihar Zamfara kamar yadda jaridar Daily Trust ta wallafa.

Salamatu ta yi wa mijinta lahani ne bayan sun samu rashin jituwa sakamakon fada mata cewa ya yana son ya yi mata kishiya.

Salamatu da dauki kujera ta buga wa mijinta a kai kuma nan take ya fadi sumame. Mutane sun garzaya dashi zuwa asibiti amma bayan kankanin lokaci sai ya ce ga garinku.

Kakakin hukumar Yan sandan jihar Zamfara, SP Muhammad Shehu ya ce wanda ake zargin tana hannun hukuma kuma ta amsa laifin da ake zargin ta da aikatawa.

“Ana cigaba da gudanar da bincike a sashin binciken masu aikata manyan laifuka (SCID) kuma nan da kankanin lokaci za’a gurfanar da ita gaban kotu. Hukumar ta amfani da wannan damar wajen gargadin mutane su dena daukin doka a hannunsu.

“A maimakon hakan, su shigar da kara a caji ofis mafi kusa dasu domin a dauki matakan da suka dace,” inji shi.

 

Related Articles

Back to top button