Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe ‘Yan Uwan Juna 3 Bayan Biyan Kudin Fansa A Taraba

‘Yansanda sun tabbadar da cewar ‘yan bindiga sun kashe wasu ‘yan uwa juna uku a karamar hukumar Lau da ke Jihar Taraba.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin rundunar ‘yansandan jihar, Abdullahi Usman, ya ce lamarin ya faru ne a ranar Lahadi a unguwar Garin Dogo da ke karamar hukumar Lau.

‘Yan uwan junan ​​uku, a cewar ‘yansanda, an yi garkuwa da su ne daga yankin.

Masu garkuwa da mutanen sun bukaci a biya su kudin fansa miliyan 100 domin su sako wadanda suka kashe ga mahaifinsu, Alhaji Musa, wanda dillalin shanu ne amma ya ce iya miliyan 60 zai iya biya kuma suka amince.

‘Yan bindigar sun bukaci a biya su tsabar kudi sannan a aike da dan acaba ya kai musu .

Sai dai daga baya sun kashe wanda ya kai kudin fansar tare da ’yan uwan junan uku bayan sun karbi kudin.

Related Articles

Back to top button