Labarai

‘Yan Daba Sun Raunata Soja Da ‘Yan Kwana-Kwana 2 Yayin Da Gobara Ta Tashi A Gidan Mai A Kwara

‘Yan Daba Sun Raunata Soja Da ‘Yan Kwana-Kwana 2 Yayin Da Gobara Ta Tashi A Gidan Mai A Kwara

‘Yan Daba Sun Raunata Soja Da ‘Yan Kwana-Kwana 2 Yayin Da Gobara Ta Tashi A Gidan Mai A Kwara

‘Yan Daba Sun Raunata Soja Da ‘Yan Kwana-Kwana 2 Yayin Da Gobara Ta Tashi A Gidan Mai A Kwara

Wasu ‘yan daba sun kai wa wani soja da jami’an kashe gobara biyu na Jihar Kwara hari tare da raunata su yayin da suke aikin ceto a wani gidan mai da gobara ta kone a Ilorin, babban birnin jihar.

An kai sojan da jami’an hukumar kashe gobara ta jihar zuwa gidan man K&R da ke unguwar Oke Agodi a cikin birnin Ilorin, domin kashe wutar da ta tashi da misalin karfe 9:30 na dare.

Amma, ‘yan daban suka fara jifan sojoji da jami’an kashe gobara inda ana haka suka jikkata soja daya da ‘yan kwana-kwana biyu.

LEADERSHIP ta tattaro cewa daga karshe sojojin sun dawo da zaman lafiya a yankin yayin da ‘yan kwana-kwana suka samu nasarar kashe gobarar.

Sai dai gobarar ta cinye motoci biyu da ofisoshi biyu kafin ‘yan kwana-kwana su kashe ta.

Kimanin kadarar Naira 21.7m aka yi asara a gobarar yayin da kiyasin dukiyar da aka ceto daga gobarar ta kai Naira 48.4million.

Kakakin hukumar kashe gobara ta Jihar Kwara, Hassan Adekunle, a wata sanarwa a ranar Laraba, ya tabbatar da barkewar gobarar da harin da aka kai kan sojoji da ‘yan kwana-kwana.

Sanarwar ta kara da cewa: “A jiya Talata 6 ga Disamba, 2022, wasu ‘yan daba a Unguwar Oke-Agodi Alfa Yahaya da ke Ilorin sun kai hari kan jami’an hukumar kashe gobara ta Jihar Kwara tare da raunata wasu jami’an kashe gobara guda biyu a gidan man K&R Petroleum Nigeria Limited.

“Daya daga cikin tawagar sojojin Nijeriya da suka zo kwantar da tarzoma su ma sun yi ta harbin kan mai uwa da wabi, hasali ma dai wannan sojan ya samu rauni.

“Saboda haka, daraktan hukumar kashe gobara ta Jihar Kwara, Prince Falade John Olumuyiwa, ya bayyana alhininsa game da faruwar lamarin tare da bayyana al’ummar yankin Agodi a matsayin masu nuna rashin godiya da rashin yaba wa kokarin ‘yan kwana-kwana.”

 

Related Articles

Back to top button
error: Content is protected !!