Labarai

‘Yan Sanda Sun Kama Wani Saurayi Bayan an Kama Shi Yana Tuka Ferrari ta Bogi

‘Yan Sanda Sun Kama Wani Saurayi Bayan an Kama Shi Yana Tuka Ferrari ta Bogi

‘Yan Sanda Sun Kama Wani Saurayi Bayan an Kama Shi Yana Tuka Ferrari ta Bogi

‘Yan Sanda Sun Kama Wani Saurayi Bayan an Kama Shi Yana Tuka Ferrari ta Bogi

Rundunar ‘yan sandan kasar Italiya sun cafke wani matashi mai shekaru 26 saboda yana tuka mota kirar Ferrari F340 ta bogi.

Matashin mai hazaka ya sauya kirar motar Toyota MR2 Coupe zuwa Ferrari din wacce zata kai tsadar £180,000.

‘Yan sandan sun ce ya zama dole ne a kare tambarin kamfanin tare da gujewa yin ta bogin bayan sun yi suna a duniya.

‘Yan sandan kasar Italiya sun kama wani matashi mai shekaru 26 kan tuka mota kirar Ferrari F430 amma ta bogi.

Kamar yadda The Sun UK suka rahoto, mutumin da ba a bayyana sunansa ba, ya mayar da motarsa kirar Toyota MR2 Coupe zuwa wata mota da tayi kama da Ferrari F430.

A wani bidiyon da yayi yawo a dandalin sada zumunta a ranar Litinin, an ga ‘yan sanda sun tasa keyar mutumin dake cikin motar.

Motar bogin ta mallaki wasu sassan asalin kirar Ferrari din. Ana zarginsa ne da yin amfani da tambarin su ba tare da izini ba bayan mai magana da yawun ofishin gurfanarwa na Asti ya kai rahoto, jaridar Vanguard ta rahoto.

An fara kera Ferrari F340 tsakanin shekarar 2004 zuwa 2009 kuma kudinta zai kai £180,000.

Mai magana da yawun Guardia di Fianza na kasar Italiya a wata takarda yace: “‘Yan sandan sun aiwatar da aikin ne karkashin jagorancin masu gurfanarwa na Asti.

“Amfanin hakan shi ne bai wa kamfanin kariya ballantana a wannan lamarin da suka jajirce wurin kawo kaya masu inganci kuma an sansu tare da yabawa duk wani tambarinsu a duniya.”

Related Articles

Back to top button
error: Content is protected !!