Yankin Arewa Maso Gabashin Nijeriya Na Bukatar Agajin Gaggawa – MDD
Yankin Arewa Maso Gabashin Nijeriya Na Bukatar Agajin Gaggawa – MDD
Yankin Arewa Maso Gabashin Nijeriya Na Bukatar Agajin Gaggawa – MDD

Ofishin Majalisar Dinkin Duniya mai kula da ayyukan jin kai a Nijeriya, ya bayyana cewa har yanzu ba a shawo kan matsalar jin kai a yankin Arewa maso Gabas ba, yayin da mata da kananan yara suka rasa muhallansu a shekarar 2022.
A cewar rahoton Majalisar Dinkin Duniya a cikin 2023, miliyoyin mutane a Njjeriya za su ci gaba da fuskantar talauci, yayin da da dama kuma za su yi ta fadi tashin neman abinci.
Arewa maso gabashin Nijeriya ya kasance daya daga cikin manyan matsalolin jin kai a duniya, inda akalla mutane sama da miliyan takwas ke bukatar agaji a shekarar 2023.
Matsalolin da mata da maza da yara ke fama da su a kowace rana a fadin Jihohin Borno da Adamawa da Yobe har yanzu na karuwa, a cewar rahoton.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce, ana bukatar kusan Dala biliyan 1.2 domin tallafawa mutane miliyan 5.4 a fadin Nijeriya.