Labarai

Yansanda Sun Cafke ‘Yan Fashin Daji 7, Sun Ceto Mutane 15

Yansanda Sun Cafke ‘Yan Fashin Daji 7, Sun Ceto Mutane 15

Rundunar ‘yansandan Jihar Zamfara ta kama wasu mutane bakwai da ake zargi da aikata laifukan da suka shafi fashi da makami ciki har da mace mai kai wa ‘yan bindiga makamai.

Sannan sun samu nasarar kubutar da wasu mutane 15 da aka yi garkuwa da su bayan shafe kwanaki 50 a hannun masu garkuwan

Kakakin Rundunar ‘Yansandan jihar, SP Muhammad Shehu, ne ya bayyana haka yayin da yake gabatar da wadanda ake zargin ga manema labarai a shelkwatar rundunar da ke Gusau a ranar Alhamis.

A cewarsa, an kama wasu mutane shida da ake zargi da laifin hada baki, da kuma tsoratarwa da karbar kudaden fansa a garuruwan yankin karamar hukumar Anka.

Wadanda ake zargin sun hada da, Jamilu Muhammad na kauyen Gadar Manya, Zayyanu Barmo na kauyen Manya Babba, Abubakar Usman na kauyen Mandau, Lauwali Girkau na kauyen Girkau, Sala Girkau na kauyen Girkau da Abubakar Yahaya na kauyen Tungar Mani.

Related Articles

Back to top button