Labarai

Yanzu Yanzu Kotu Ta Yankewa Abduljabbar hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya

Yanzu Yanzu Kotu Ta Yankewa Abduljabbar hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya

Bayan sama da shekara daya ana kai ruwa rana a kotun shari’a dake jihar Kano, an zo karshe a yau Alhamis, 15 ga watan Disamba, 2022.

Alkalin kotun ya karanto jerin laifukan da kotu ta kama Malam Abduljabbar da su kuma ya yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Mai shari’a Sarki Yola ya tabbatar da duk maganganun da Abduljabbar yake yi shi ya kirkira kuma ya jinginawa ma’aiki (SAW).

Mai shari’a ya tabbatar da cewa maganganun fassara hadisan manzon Allah da Abduljabbar yace kage ne ko jingina ne, karya yake kuma hasali ma shine ya jingina kalmomin ga Ma’aiki.

A cewar Alkali:

“Sashi na ɗati uku da sittin da uku sashin (f) ya bada hukunci haka:
An yankewa Abduljabar hukuncin kisa Ta hanyar rataya
Sashi 380 ne ya bada wannan hukuncin ta hanyar rataya
Kuma kotu ta kwace litttafansa da ya gabatar da su a gaban kotu dan sheda
Kuma kotu ta bada umarnin kwace masallatansa gudu biyu Na filin Mushe dana Unguwar sabuwar Gwandu.”

Alkalin ya kara da cewa Kotu ta umarci hani da saka karatunsa a Gidajen radio, Gidajen Talabijin Da kafafen sadarwa.

Hakazalika Kotu ta bashi damar daukaka kara nan da kwana 30.

Sheikh Abduljabbar Kabara, gabanin yanke masa hukunci ya fara fadawa Alkali kotun maganganu kuma yace alkali karya yake masa.

Ba tare da bata lokaci ba jami’ai suka dakatar da shi daga maganganun kuma aka tafi hutu.

Related Articles

Back to top button