LabaraiSiyasa

Zaben 2023: Buhari Ya Hori Jami’an Tsaro Su Zama ‘Yan Ba Ruwanmu A Siyasa

Zaben 2023: Buhari Ya Hori Jami’an Tsaro Su Zama ‘Yan Ba Ruwanmu A Siyasa

Zaben 2023: Buhari Ya Hori Jami’an Tsaro Su Zama ‘Yan Ba Ruwanmu A Siyasa

2023: Buhari Ya Hori Jami’an Tsaro Su Zama ‘Yan Ba Ruwanmu A Siyasa

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bukaci Jami’an Tsaron Nijeriya da su zama ‘yan ba ruwan mu, su kauracewa shiga harkokin siyasa tare da ci-gaba da aiki a bisa ga kundin tsarin mulkin Nijeriya domin tabbatar da nasarar Babban Zaben 2023.

Da yake bude Babban Taron Shugaban Rundunar Soji na 2022 yau a Sakkwato, Buhari ya yi kira ga jami’an soji da su ci-gaba da mutunta ‘yancin dan -Adam a yayin kai farmaki a karkashin tsarin da duniya ta aminta da shi.

Shugaban ya yi alkawalin ci-gaba da kokarin kara zamanantar da Rundunar Tsaro ciki har da inganta fannin sha’anin jiragen sama na jami’an sojin Kasa.

A kan sha’anin Babban Zaben 2023, Shugaba Buhari ya bayyana cewar jami’an soji da Rundunar Tsaro bakidaya suna mutunta farar hula ta hanyar bayar da ingantaccen yanayin gudanar da zabe lafiya.

Ya nuna jin dadinsa kan yadda Shugaban Rundunar Soji ya gabatar da bitar ka’idoji da dokokin da sojoji za su yi aiki da su a yayin zaben 2023 yana cewar akwai bukatar sojojin su maimaita kwarewar da suka nuna a zabukan Jihohin Anambra, Ekiti da Osun.

A kan Babban Taron sojojin na bana kan bitar nasarorin da kalubalen da aka samu a 2022 da shirin tunkarar 2023, Buhari ya kalubalanci sojojin da su himmatu wajen bitar nasarorin da aka samu su kuma tabbatar da dorewar su domin bunkasa tsaro a fadin Kasa.

A jawabinsa Shugaban Rundunar Sojojin Kasa, Laftanar – Janar Faruk Yahaya ya bayyana cewar Sojojin Nijeriya sun samu gagarumar nasarar kawar da ta’addanci da shawo kan matsalolin tsaro a sassan Kasar nan bakidaya.

Ya ce daga Arewa- Maso- Gabas zuwa Arewa- Maso Yamma, zuwa Kudu- Maso Gabas da Kudu- Maso- Yamma duka sun taka muhimmiyar rawar ganin tabbatar da tsaro a fadin Kasa tare da taimakon makwabtan Kasashe ta hanyar hanawa ‘yan ta’adda cin karensu ba babbaka.

Shugaban Sojojin ya kara da cewar dimbin manyan makamai, bindigogi da harsasai da suka samu nasarar kwatowa a hannun ‘yan ta’adda ya karawa Rundunar Sojojin Nijeriya kwarin guiwa sosai.

Ya kuma ce sun bayar da muhimmanci sosai ga kula da walwala da jin dadin sojoji, fitowa da tsarin ba da bashi da dama tare da gyaran barikin sojoji domin inganta jin dadin su.

A jawabinsa mai masaukin baki, Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na Jihar Sakkwato ya godewa Buhari kan halartar taron tare da yabawa kokarin da Rundunar Soja da dukkanin Shugabannin Hukumomin Tsaro ke yi wajen tabbatar da ingantaccen tsaro a Sakkwato da Arewa Maso-Yamma bakidaya.

Ya ce Gwamnatinsa ta na bayar da dukkanin gudunmuwa da cikakken goyon baya ga jami’an tsaro a fadin Jihar. Ya ce Gwamnatinsa ta kara adadin alawus din da take baiwa jami’an tsaro zuwa kashi 150% domin kara masu kwarin guiwa.

Related Articles

Back to top button