Lafiya

Maganin Infection Na Mata Sadidan

Maganin Infection Na Mata Sadidan

Dukkan wata matsala ta sanyin mara kama daga sanyin mara (vaginities/toilet infections, UTI & STDs), yoyon fitsari, ‘kululun mahaifa (fibroid), da sauran cututtukan al’aura na daga cikin abubuwan da ka iya hana mace jin dadin jima’i.

Misali, sanyin gaba mai zuwa da ‘yan ‘kananan kuraje cikin farji , na sanya mace taji zafi wajen jima’i yayinda zakari ke kai-kawo cikin farji, wanda sau da yawa masu kurajen basu ma san suna da kurajen ba cikin al’aura, saidai suce suna jin zafi lokacin saduwa.

Kurajen suna fashewa saboda da gugar zakari, sai wurin ya zama rauni. Hakan nasa mata tsoron jima’i da ganinsa abin azabtarwa gare su mai maimakon abin jin dadi. Sau tari basu san abinda ya haddasa zafin ba, wanda kuma mai yiwuwa ciwon sanyi.

Ciwon sanyi na iya dakushe sha’awar mace ko namiji. Ciwon sanyi na iya haddasa bushewar gaba (vaginal dryness) wanda alamunsa shine daukewar ni’ima da ‘kaikayin gaba. Idan gaba ya bushe zaiyi wahala mace da miji suji dadin jima’i in banda zafi.

Haka kuma shima ‘kululun mahaifa (fibroid) yakan ci karo da zakari cikin farji sai mace taji wani irin yanayi marar dadi (discomfort) lokacin nishadin aure. Kuma yana danne mahaifa ya hana haifuwa da kuma sanya yawan zubar jini. Don haka neman magani shine mafita.

Kada kumanta Kudanna mana Alamar kararrawar sanarwa domin samun jin kararrawar sanarwar shirye-shiryenmu Masu ƙayatar wa mungode.

Back to top button