Siyasa

Idan da ace ba na takarar shugaban kasa, ba zan zaɓi Atiku ko Obi ba don ba su cancanta ba – Tinubu

Ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC Bola Tinubu ya bayyana cewa da Atiku Abubakar na PDap da Peter Obi na LP, ba su cancanci kuri’ar sa ba da ace ba shi cikin ƴan takarar shugaban Kasa.

Tinubu ya yi wannan ikirarin ne a lokacin da yake tattaunawa da BBC a birnin Landan bayan jawabi da yayi a cibiyar Chatham Hause dake birnin Landan.

Da aka tambayeshi ko yaya yayi ya tara biliyoyin naira da ake masa gani da ikirarin hamshakin attajiri ne, da wasu ke zargin daga aljihun gwamnatin Legas ne ya ke tara waɗannan kuɗaɗe da har ya zama gagarimin attajiri.

Tinubu ya ba da amsar cewa ” Arzikin da nake da shi na wane kuma ya samo asaline daga waɗanda na gada daga Iyaye. Daga nan na bunƙasa shi har na samu tarin dukiyar da nake da shi yanzu.

Da aka tambaye shi ko me zai yi daban da yadda shugaban Kasa Muhammadu Buhari yayi, ganin sun fito jam’iyya ɗaya sai Tinubu ya ce ” Matsalar tsaro da bunkasa tattalin arzikin kasa sune zan fara saka wa a gaba. Kuma zan yi su ne a matsayina na Bola Tinubu. Wanda shine banbancin dake tsakanina da Muhammadu Buhari.

Tinubu ya ce zai kara yawan jami’an tsaron kasar nan idan ya zama shugaban kasa.

” Yadda na bunkasa jihar Legas, jihar ta yi karfin da za ta iya tsayawa da ƙafafuwanta kamar kasa mai cin gashin kanta a Najeriya.

Related Articles

Back to top button