Siyasa
Masu Son Gwamnatin Tarayya Ta Yi Magudi A Zaben Bauchi, Ba Za Su Yi Nasara Ba – Bala Mohammed
Masu Son Gwamnatin Tarayya Ta Yi Magudi A Zaben Bauchi, Ba Za Su Yi Nasara Ba – Bala Mohammed
Masu Son Gwamnatin Tarayya Ta Yi Magudi A Zaben Bauchi, Ba Za Su Yi Nasara Ba – Bala Mohammed

Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed ya yi zargin cewa ana yunkurin yi masa magudi a zaben gwamnan da za a gudanar a 2023
Ya bayyana haka ne ranar Lahadi a gidan gwamnatin Jihar Bauchi yayin da kungiyar Kiristoci ta jihar ta kai masa ziyarar bikin Kirsimeti.
Arewa top ta ambato Gwamna Bala Mohammed yana cewa mutanen da suke yunkurin yin amfani da karfin gwamnatin tarayya domin yin magudin zabe ba za su yi nasara ba.
Ya ce Shugaba Muhammadu Buhari ba zai bari hakarsu ta cimma ruwa ba.
Bala Mohammed zai kara da dan takarar jam’iyyar APC, Siddique wanda tsohon babban sojan saman Nijeriya ne.